Ɗan takardar zaben shugaban ƙasa a 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi fatali da tsarin karɓa-karɓa a matsayin maganin magance rigimar shugabancin Najeriya.
Atiku ya ce tsarin tsarin karɓa-karɓa ba shi ne matsalar Najeriya ba, kuma ba shi ne tsarin da zai warware matsalar Najeriya ba.
Akwai wasu a cikin manyan jam’iyyar da ke rajin cewa a maida takardar shugaban ƙasa a ɓangaren kudancin ƙasar nan.
To sai dai kuma Atiku Abubakar wanda tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa a gwamnatin Olusegun Obasanjo, bai goyi bayan tsarin karɓa-karɓa.
Ya yi wannan raddi ne a Taron Kwamitin Dattawa na 94 da PDP, jam’iyya mai mulki, wanda aka gudanar a ranar Alhamis, a Abuja.
“Jam’iyyar PDP na da ‘yancin gindaya yadda za a tafiyar da ita. Su kuma ‘yan Najeriya su na da ‘yancin zaɓen wanda su ke ganin yada ce.
A kan bin tsarin karɓa-karɓa wajen bayyana ko daga wace shiyya ɗan takarar muƙamin shugabancin jam’iyya zai fito kuwa, Atiku ya ce, “zan so na ga matasa da mata sosai cikin shugabannin jam’iyyar da za a yi ba da daɗewa ba.
Ya ce tsarin da PDP za ta zartas yau shi ne zai tantance ko jam’iyyar za ta yi nasara a zaɓen 2023, ko ba za ta yi ba.
Atiku A Kan Takarar Shugaban Ƙasa Ƙarƙashin PDP a zaɓen 1999 Da 2003:
Atiku ya ce an zaɓi Olusegun Obasanjo ne takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP, sakamakon rashin adalcin da ya ce an yi wa M.K.O Abiola, inda shugaban lokacin ya soke zaɓen da ya ci.
“A zaɓen 2003 dukkan gwamnonin PDP sun same ni a Villa su ka ce ba za su tsaida Obasanjo ba, ni za su tsayar. Ga Maƙarfi nan a zaune, shi ne shaida, domin a lokacin ya na gwamna, kuma da shi aka ɗunguma su ka same ni.
“Sai na ce masu a’a, ba za a yi haka ba. Na nuna masu abin da Kwamitin Dattawa na PDP ya amince cewa ɗan kudu zai riƙe mulki tsawon shekaru 8. Daga nan aka wuce wurin.” Inji Atiku.