Hukumar kwastam ta ƙasa dake jihar Katsina ta zargi ‘yan sumoga da yi wa yaki da ‘yan bindiga a jihar kafar angulu.
Shugaban hukumar Wada Chedi ya sanar da haka a wata takarda da ta fito daga ofishinsa a farkon wannan mako.
Jihar Katsina na cikin jihohin yankin Arewa maso Yamma dake fama da hare-haren ‘yan bindiga a kasar nan.
A dalilin haka gwamnati ta dauki wasu tsauraran matakai domin hana aiyukkan maharan da samar da tsaro wa mutane a jihar.
Rufe wasu kasuwani, hana siyar da mai a galan ko jarka, hana safarar dabbobi a mota, toshe layukan sadarwa da rufe hanyoyi a jihar na daga cikin matakan da gwamnati ta dauka.
Yadda ‘yan sumoga ke yi wa yaki da mahara kafar angulu
Chedi ya ce rundunar kwastam ta kama motoci da babura da aka canja tankunan mansu zuwa masu girma domin su iya dakon fetur da yawa.
Ya ce rundunar ta gano cewa ‘yan sumogal na amfani da wadannan ababen hawa suna siyan fetur domin siyar wa ‘yan bindiga.
“Mun bi sawunsu domin kama su amma tun da suka ankare jami’ai na binsu su sai suka gudu suka bar ababen hawan.
“Mun kama motoci biyu kiran Peugeot 504 da wasu babura da aka cansa tankin man su amma har yanzu bamu gano inda ‘yan sumogal da ‘yan bindigan ke haduwa suna cinikin man ba.
Chedi ya ce hukumar ta bi kauyukan dake kusa da iyakan ƙasar nan a jihar tana wayar wa mutanen kauyukan sanin mahimmancin hada hannu da hukumar Kwastam domin hana aiyukkan ‘yan sumogal a jihar.
Ya kuma musanta zargin da mutane ke yi na cewa hukumar ta boye direban da ya kashe mutane a Jibia da sunayen ma’aikatan hukumar da suka harbe wani mutum a Fadi Gurje dake Mani.
Discussion about this post