Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu ‘yan banga biyu dake da hannu a kisar wani barwon babur a karamar hukumar Gwaram.
Kakakin rundunar Lawan Adam ya sanar da haka a makon jiya a garin Dutse.
Adam ya ce rundunar ta kama wadannan mutane a kauyen Kila kuma tuni har an fara gudanar da bincike a kansu.
Ya ce rundunar ta samu labarin abin da ya faru bayan kiran da aka yi musu ranar Lahadi da karfe biyar na yamma.
” Jami’an ‘yan sanda sun iske barawon babur din kwance malemale cikin jini mutane tsatstsaya a kan sa a lokacin da suka isa wurin da abin ya faru.
“Ko da muka kai mutumin asibitin Gwaram Cottage likita ya tabbatar cewa ya mutu.
Adam ya ce ‘yan bangan su biyu na tsare a ofishin ‘yan sanda.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Aliyu Tafida ya bada umurnin kai fayil din dake kunshe da abinda ya faru zuwa fannin gurfanar da masu aikata laifufa irin haka.
Idan ba a manta ba a ranar Larabar makon jiya kungiyar ‘yan banga sun kashe mutum 12 a kasuwan Mande dake karamar hukumar Gwadabawa jihar Sokoto.
Hakan ya sa ‘yan uwan mutanen da aka kashe suka kawo harin ramuwar gayya inda mutum 20 suka mutu a Ungwan Mai Lalle dake karamar hukumar Sabin Birni ranar Juma’a.
A takaice dai mutum 32 ne aka rasa a jihar tsakanin ranar Laraba da Juma’ar makon jiya.
Gwamnatin jihar da rundunar ‘yan sanda basu ce komai ba akai tukunna, sai dai kwamishinan harkokin tsaron jihar Garba Moyi ya ce rashin kiyaye dokar hana cin kasuwannin mako-mako da gwamnati ta saka ya sa abin ma ya faru.