” Na fito daga Abuja ne zan tafi garin Gusau. Kafin mu isa sai muka iske an tare hanya motoci tsatstsaye. Aka ce mana wai ‘yan bindiga ne suka tare hanyar. A lokacin mun wuce kauyen ‘yankara dake karkashin jihar Katsina kenan. Ni da kaina na taya ‘yan sanda kwashe gawarwakin Sojojin da ‘yan bindigan suka kashe.” In ji wani direba da ya taso daga Abuja za shi garin Gusau.
Ita kuwa Maryam Gatawa, malama a jami’ar gwamnatin Tarayya dake jihar Zamfara, ta ce ko da suka iso wurin da ‘yan bindigan suka yi garkuwa da mutane, sun iske kauyawa na ta guje-guje wasu na dannawa cikin daji.
” Maharan sun Kashe Sojojin da suka yi arangama da ‘yan bindigan.” In ji Maryam.
Jihar Zamfara na ci gaba da fama da hare-haren yan bindiga duk da matakan da gwamnati ta saka domin dakile ayyukan maharan.
Maharan sun tare hanyar zuwa garin Gusau a tsakanin kauyukan Wanzamai da Kucheri daka karamar hukumar Tsafe.
Da rana tsaka da misalin karfe 2 na rana suka tare hanyar. Sun dauki tsawon minti 30 suna dibar mutane da arangama da sojoji
da suka yi.
Abin yayi muni matuka da har maharan sun kashe jam’ai. Ba a san ko mahara nawa kashe ba.
Discussion about this post