Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutanen da ba a san yawan su ba kuma sun yi garkuwa da mutum bakwai a kauyen Mazakuka dake karamar hukumar Mashegu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Monday Kuryas Wanda ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Litini ya ce maharan sun far wa masallata ne a masallacin Asuba.
Monday ya ce maharan sun cinanwa dukiyar wani Alhaji Abubakar Maigandus wuta.
Sai dai jami’an tsaron ‘yan sanda sun kashe mutum daya daga cikin maharan.
Monday ya ce ga dukan alamu wannan harin daukar fansa ne mahara suka kawo wannan kauye.
Ya ce runduna ta aika da ma’aikatan domin samar da zaman lafiya a kauyen.
Monday ya yi kira ga mazaunan karkara da su taimaka wa ‘yan sanda da bayanan sirri da za su taimaka wajen kama wa da hukunta masu tada zaune tsaye a jihar.