Wasu ‘yan bindiga sun kutsa zauren taron sarakunan gargajiya, inda su ka buɗe wa mahalarta taron wuta, tare da bindige basarake biyu.
Mummunan al’amarin ya faru a Nnenesa, cikin Ƙaramar Hukumar Njaba a Jihar Imo.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Imo, Mike Abattam ya tabbatar da kisan sarakunan gargajiya ɗin, da su ka haɗa da E. Duruebere na Masarautar Okwudor sai kuma Samoson Osinwe na Masarautar Ihebinewerre.
Wani da ba ya so a bayyana sunan sa, ya shaida wa wakilin mu cewa ‘yan bindigar sun buɗe wuta a cikin majalisar gungun sarakunan, kuma bayan sun yi kisa da raunata wasu, sai su ka fice su ka yi tafiyar su.
Har yanzu dai babu wata ƙungiya da ta fito ta yi shelar kai harin.
Jihar Imo na cikin jihohin Kudu maso Gabas, inda ake fama da tashe-tashen hankula kan kartar ƙasar da tsagerun IPOB ke yi wajen neman kafa Biafra.