Idan ba a manta ba hukumar EFCC na neman uwargidan gwamnan Kano, Hafsat Ganduje dominnta bayyana a gabanta don amsa wasu tambayoyi game da zargin rashawa kan kuɗaɗen wasu filaye tsakaninta da ɗanta.
Abin kamar almara ɗanta da kansa ne ya ya rubuta wa hukumar EFCC wasikar lallai ta binciki mahaifiyarsa kan sama da faɗi da tayi da miliyoyin naira kudaden harƙallar wasu filayen gwamnatin Kano da tayi.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin wannan badaƙala a cikin watan Satumba.
Sai dai kuma maimakon Hafsat Ganduje ta amsa gayyatar sai ta ki, kwanaki biyu bayan bayyanar labarin sai aka gan ta can a ƙasar Birtaniya ta tafi bikin sauka karatun ɗanta da ya kammala digiri a jami’ar ƙasar.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa tun da misslinkarfe 6 na yamman Litinin ta ke tsare a EFCC din har zuwa safiyar Talata.
Da safiyar Talata aka sake ta.
Discussion about this post