Bayan kaurin sunan da ya yi a matsayin shafin da ke taimakawa wajen yada jita-jita, da bayanan karya da ma irin sharhunan da ke tayar da rikici, shafin tiwita ya kasance kan gaba cikin shafukan da yawancin masu amfani da shafukan sada zumunta ke samun damar yin mahawara.
Wannan sauyin ya fara ne tun bayan da shugaban kamfanin Jack Dorsey ya kafa kamfanin da abokan shi wadanda suka hada da: Noah Glass, Biz Stone, Evan Williams a shekarar 2006.
Daga samar da dandalin gudanar da harkokin sada zumunta zuwa hanyar sadarwa da fadan albarkacin baki, tiwita ya shafe shekaru da dama ya na kyakyawar sauyi da ma kara yawan masu amfani da dandalin a duniya baki daya.
Tiwita yana da burin kasuwanci, a shekarar 2020 kadai kamfanin ya sami kudaden shiga da suka kai dalan Amirka biliyan 3.7. Wannan dandalin na kuma samar da ayyukan yi ga dimbin yawan mutanen da ke amfani da shi wajen yin tallata hajojinsu.
Bisa bayanan Statista, wani kamfanin Jamus da yak ware wajen tantance alkaluman kasuwanni da masu saye da ma amfani da kayayyakin masarufi, ya ce a shekarar 2019, kowani wata adadin masu amfani da shafin tiwita akai-akai yak an kai milliyan 290.5 kuma ana hasashen wannan adadin zai kai milliyan 340 a shekakar 2024.
Tiwita, sanya ido kan labarai a zamanin aikin jarida a yanar gizo
Tiwita ya dade yana alfahari da kan sa a matsayin “taga na ganin abin da ke faruwa a duniya.” A aikin jarida da sauran ayyukan da suka shafi kafofin yada labarai sauyin da kamfanin ya fiskanta ya kawo wasu karin suaye-sauye a aikin masu dauko labarai, editoci, da ma al’adar dakunan labarai na gargajiya.
Bayan haka, a wani abin da ake ganin abin yabo ne, dandalin, ta hanyar jadadda mahimmancin ‘yancin fadar albarkacin baki ya kasance dalilin bunkasar aikin jaridar “‘yan kasa”. Wannan ya bai wa ‘yan kasa damar kawo rahotannin abubuwan da ke faruwa a yankunansu ta yin amfani da gajerun sakonni, da hotuna da bidiyo.
Duk da cewa wannan ya kawo jama’a kusa da kafafen yada labarai a hannu guda, a dayan hannu ya janyo yaduwar labarai marasa gaskiya.
Ga ‘yan jarida wannan dandalin na taimaka musu wajen yada labaransu da ma damar ma’amala da ma’abotan shafukansu.
Shafin na tiwita yana baiwa ‘yan jarida damar samun majiyoyi masu nagarta ba tare da sun fita sun je wurin da abubuwa ke faruwa ba.
Kungiyoyin siyasa, ma’aikatun gwamnati da manyan ‘yan wasa na amfani da shafin tiwita domin hulda da ma’abotan shafukansu. Wannan ya kuma taimaka wa ‘yan jarida wajen samun sanarwa da ma sauran bayanai masu mahimmanci.
Yayin da take bayani kan rawar da tiwita ke takawa a wani labarin da ta yi wa taken “Yadda ‘yan jarida za su iya hulda mai mahimmanci da ma’abotansu” ‘yar jarida Jennifer Hollett ta jaddada mahimmancin da dandalin ke da shi wajne sanya ido kan labarai da majiyoyi.
A cewar ta “A tiwita ake samun labari da dumi-dumin shi.” Dan haka, ita ce babbar kafar yada labarai a cikin kasa, wanda zai kawo ma jama’a labari yayin da yake faruwa.”
Ba kamar sauran kafofi na gargajiya ba irin su talbijin da jarida, a shafin tiwita mutane na iya mayar da martani kai tsaye su tattauna da ‘yan jarida a tiwitan.
“mutane za su fi mayar da martani ga ‘yan jaridan da za su amsa tambayoyinsu da wadanda za su ba su shawarwari. Wannan zai kara yawan masu amfani da shafin, kuma zai ja hankalin ga ayyukan dan jaridar, a cewarta.
Yada labarin ta yin amfani da “thread”
Tun da tiwitar ta takaita yawan kalmomin da za’a iya rubutawa a lokaci guda, ta samar da abin da take kira “Thread” wanda salo ne na rubuta sharhi daki-daki ana amfani da gajeren sakin layi a kowani daki domin kada a wuce adadin kalmomin da ya kamata.
Ga ‘yan jarida, wadannan gajerun sakin layin na da mahimmanci wajen bayyana labaran da ke da sarkakiya. Avery Friedman, wani dan jarida ya rubuta wani labari mai taken “Yadda ‘yan jarida da dakunan labarai za su iya amfani da threads wajen inganta rahotanni.” Friedman ya ce Threads za su taimaka wajen bayana gaskiyar labari yayin da yake faruwa.
Ganin cewa thread yana dadewa sosai, ‘yan harida na iya amfani da shi wajen bayar da babban labari su kuma danganta shi da ainihin tarihin shi. Wannan na nufin ‘yan jarida na iya amfani da shi wajen nuna tarihin labaran da suka yi a baya ko kuma su haskaka ayyukan ‘yan jaridan da suka yi aiki a baya.
Tweeterdeck: Hanyar sanya ido mai mahimmanci ga shafin tiwita
Daya daga cikin manyan abubuwan da ‘yan jarida ke cin moriyar shi a tiwita shi ne Tweeterdeck. Shekaru 13 da suka gabata aka kirkiro shi kuma ana amfani da shi ne wajen ingantawa da zaben abubuwan da mai shafi ke bukata a shafin shi ko shafin ta.
Tweeterdeck na da ginshikai da layukan da za a iya shiryawa a shafin ta yadda mai amfani da shafin zai ga duk sadda aka ambace shi, da sakonni na kai tsaye, jerin abubuwan da ke faruwa, abubuwan da mai shafi ya fi sha’awa, bincike, hashtags, da duk abin da mai shafin ya rubuta.
Masu amfani da tiwita suna iya sa ido kan shafuka da dama a lokaci guda. Wannan na nufin ‘yan jaridan da ke amfani da shafin na iya samun labari da zarar aka sanya a shafin.
Babban alfanun tweeterdeck shi ne na samun labarai da dumi-duminsu. Tun da hukumomin gwamnati ma can tiwita, a nan ne yawanci ke wallafa sanarwar manema labarai ta yadda ‘yan jarida za su samu kai tsaye.
A karshe
Tiwita na taka muhimmiyar rawa a kan irin sauyin da ake gani a aikin jarida musamman yanzu da ake amfani da dijital mediya wanda ke daukar hankalin masu karatu. An tsara dandalin yadda zai inganta aikin ‘yan jarida ya kara musu yawan ma’abota ya kuma hada su da jama’a daga duniya baki daya masu majiyoyi masu nagarta.
‘Yan jaridan da ke amfani da tiwita lallai za su sami cigaba mai amfani sai dai dole su yi hattara wajen tantance majiyoyi domin su guji fadawa tarkon labaran karya wato “fake news”