Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da mataimakin sa Namadi Sambo duk ba su halarci taron gangami na PDP ba.
An yi taron zaben sabbin shugabannin jam’iyyar PDP ranar Asabar a Abuja, babbar birnin tarayyar Najeriya.
Sai dai kuma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da mataimakin sa duka su biyu ba su halarci taron ba.
PREMIUM TIMES ta bi diddigin sanin dalilan da ya sa duka jigajigan biyu ba su halarci taron ba in da ta gano wai yana da taro ne a ƙasar Kenya wanda ya shafi haɗin kan nahiyar Afirka.
PREMIUM TIMES ta jiyo daga majiya cewa gwamnonin Bayelsa da na Oyo, Diri da Makinde sun roki shugaba Jonathan ya halarci taron in ya so bayan ya bayyana koda na mintoci ne sai ya yi tafiyarsa amma ya ki.
Makinda da Diri sun yi masa alƙawarin za su shirya masa jirgin da zai tafi da shi can kasar Kenya ɗin bayan taron PDP amma kememe ya ki halarta ya kama gaban sa.
Gwamnan jihar Bayelsa Diri, ya same Jonathan tun kafin ranar gangamin ya roke shi ya jagoranci tawagar deliget ɗin jihar amma ya ki.
Wani jigo a jam’iyyar PDP ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa da gangar Jonathan ya ki halartar taron PDP ɗin. Ya ce ba tun yanzu ba tsohon shugaban Ƙasa Jonathan ya ke kauce wa duk wani abu da ya shafi Jam’iyyar. Ba zai zo ba kuma ba zai aika da wakili ba.
Haka shima mataimakin sa Namadi Sambo, shima ba a ga wulkawarsa da tawagar ƴan Kaduna ba a wurin wannan gangami.
Sai dai kuma akwai zantuttuka dake yawo cewa akwai yiwuwar Jam’iyyar APC ta tsaida Jonathan yayi mata takara a 2023.