A daidai lokacin da ake fama da matsanancin tsadar kayan abinci da kayan masarufi a Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Ma’aikatar Harkokin Noma ta farfaɗo da Hukumar Kula da Tara Abinci ta Ƙasa, domin magance matsalar ƙarancin abinci nan gaba.
Buhari ya bayar da wannan umarni a ranar Juma’a, lokacin da ya ke jawabi a ranar murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yanci.
Buhari ya yi wannan jawabi ne a daidai lokacin da miliyoyin jama’a ke ganin babu wata dabara, sai fa a samu sassaucin kayan abinci kawai.
PREMIUM TIMES Hausa ta gano cewa kwanon garin filowa da watanni biyu da su ka wuce ake sayarwa Naira 650 zuwa Naira 700, yanzu ya kai Naira 1,000.
A cikin jawabin Buhari, maimakon ya fito da tsare-tsaren yadda za a samu sauƙin kayan abinci, sai ya ɗora laifin tsadar kayan ga matsakaitan ‘yan kasuwa. Ya ce su ne ke ɓoye kaya don su yi tsada.
Idan ba a manta ba, shekaru haka Buhari ya bayyana shekaru 37 da su ka gabata, a lokacin da kayan abinci su ka riƙa gagarar ‘yan Najeriya saye a zamanin mulkin sa na soja.
Buhari a jawabin sa na ranar Juma’a, ya umarci Ma’aikatar Harkokin Noma da jami’an tsaro da Majalisar Tarayya su fito da hanyoyin magance masu ɓoye kayan abinci.
Da ya ke sake nanata ƙudirin gwamnatin sa na fitar da mutum miliyan 100 cikin ƙarfin talauci, Buhari ya ƙara kaɗa gangar fitar da mutum miliyan 100 cikin talauci, talakawa ba su tashi sun taka rawa ba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jaddada alwashin da ya ɗauka cewa gwamnatin sa za ta fitar da mutum miliyan 100 a cikin ƙangin talauci, a cikin shekaru 10.
Duk da cewa masu sukar Buhari na ganin cewa mafarki ne kawai ya ke yi da farfaganda, Buhari ya ce wannan alwashi zai iya tabbata.
Haka ya furta a cikin jawabin sa na murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yanci.
Buhari ya yi wannan jawabi a lokacin da matsalar tsaro ke ƙara jefa miliyoyin jama’a cikin halin ƙunci, mutanen karkara ke hijira zuwa birane saboda hare-haren ‘yan bindiga.
Sannan kuma ‘yan bindiga na ci gaba da jefa mutane cikin ƙangin talauci su na ƙwace miliyoyin kuɗaɗe a hannun su da sunan kuɗin fansa.
Yankuna da dama an daina noma, kuma an daina zirga-zirga a hanyoyi da yawa.
Daidai lokacin da Buhari ke jawabin, miliyoyin mutanen karkara sun daina cin kasuwannin mako-mako a wasu jihohin Arewacin ƙasar nan.
Haka kuma a kullum kayan abinci sai ƙara tsada ya ke yi a ƙasar nan.
Haka kuma Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS), ta ce akwai matalauta masu fama da ƙuncin rayuwa har mutum miliyan 82.9 a Najeriya.
Adadin na nufin kashi 40 bisa 100 na ‘yan Najeriya ba su ƙarfin su fita su yi barace-barace ba.
Discussion about this post