Ministan Harkokin Shari’a Abubakar Malami ya nesanta kan sa ko hannun ma’aikatar sa daga farmakin da jami’an ‘yan sanda su ka kai gidan Mai Shari’a Mary Odili ta Kotun Ƙoli a Abuja.
Cikin wata sanarwa da Umar Gwandu wanda shi ne Kakakin Yaɗa Labarai na Minista Malami, ya bayyana cewa, “dirar mikiyar da jami’an tsaro su ka yi a gidan Mai Shari’a Mary Odili, akwai alamu na tantagaryar iskanci wajen ƙalla shirin.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Mary Odili ta ce ba ta yarda a shiga gidan ta ba sai da sammaci daga kotu, kuma gidan ta ba gidan mijin ta ba ne, Peter Odili, wanda ke da matsala da EFCC.
Malami ya bayyana cewa yadda aka yi asarƙakar bayanai a gaban kotu har aka bada umarnin tura jami’an tsaro a gidan, akwai tantagaryar iskanci a lamarin.
Tantagaryar Iskancin Da Ke Cikin Bayanan Kai Farmaki Gidan Babbar Mai Shari’a Mary Odili -Minista Malami
“A takardar an rubuta “Joint Panel Recovery”. Kuma babu wani kwamiti mai wannan sunan a Ma’aikatar Shari’a.”
“Mu na dai da “Assets Recovery and Management Unit”, wato Sashen Kula da Dukiyar da Aka Ƙwato.” Kuma shi wannan sashen babu ruwan sa da shirya kai farmakin kamo wani.”
“Bayanin da ke ƙunshe na aikin binciken da ake yi na Kwamitin Lura da Asusun Bogi, Masu Kwarmaton da Aikin Ƙwato Kadarori Da Kuɗaɗen Sata”, shi ma duk bige ne.
“I-mel ɗin da ke kan takardar ba lambar i-mel ɗin Ma’aikatar Harkokin Shari’a ta Tarayya ba ne.
“A takardar an rubuta “Ma’aikatar Shari’a” kawai. Ba a tantance shin ‘ta jiha’ ce ko ‘ta tarayya’ ba.
Daga nan Minista Malami ya ce za a bincika domin a bankaɗo waɗanda su ka kitsa wannan tantagaryar iskanci.
Ba EFCC Ce Ta Kai Farmaki Gidan Mary Odili, Mai Shari’a Ta Kotun Ƙoli Ba -Bawa
Hukumar EFCC ta bayyana cewa danganta farmakin da wasu jami’an tsaro su ka kai gidan Mai Shari’a Mary Odili ta Kotun Ƙoli, ƙarya ce don kawai a kawo saɓani tsakanin ɓangaren Shari’a da EFCC.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran EFCC, Wilson Awujeran ya fitar ga manema labarai a ranar Juma’a da dare, kuma ya turo wa Premium Times, ya ce jami’an EFCC ba su kai farmakin ƙoƙarin yin bincike gidan Mary Odili ba.
Jiya Juma’a da dare ne dai jami’an tsaro su ka kewaye gidan Mary Odili, amma jami’an tsaron gidan ta su ka ce ba za su shiga ba, sai da sammacin kotu.
Mary Odili dai ita ce matar tsohon gwamnan jihar Delta Peter Odili, wanda ya shafe shekaru da dama ya na kulli-kurciya da EFCC. Tun bayan saukar da gwamna cikin 2007 ya ke garzayawa kotu ana ba shi kariyar hana EFCC su bincike shi ballantana a gurfanar da shi.
Wasu rahotanni sun nuna cewa Mary Odili ta shaida wa jami’an tsaron cewa ba za ta bari su shiga gidan ta ba, saboda ba gidan mijin ta Peter Odili ba ne, gidan ta ne.
Kakakin SSS Peter Afunanya, ya shaida wa Premium Times ta saƙon tes cewa, “ba SSS ne su ka dira gidan ba.”
Amma wata majiya a Kotun Ƙoli ta jajirce wa Premium Times cewa lallai SSS ne su ka kai farmakin.