Baban Hafsan Sojojin Saman Najeriya Oladayo Amao, ya bayyana cewa amfani sabbin jiragen yaƙin nan samfurin Super Tucano da Najeriya ta sayo kwanan nan, ba zai iya kakkaɓe ‘yan bindiga ba.
Amao ya ce za a iya yin nasara a kan su ne sai idan an haɗa da hare-haren sojojin ƙasa.
Amao ya yi wannan ƙarin haske a ranar Laraba a Abuja, lokacin da ya yi ganawa da wasu editocin wasu jaridun ƙasar nan.
Cikin watan Satumba Najeriya ta karɓo jirage shida samfurin Super Tucano, waɗanda ta sayo daga Amurka.
Dama kuma an aiko da wasu shida na farko tun a cikin watan Yuli.
An dai kashe dala miliyan 469.4 wajen sayo jiragen.
Amma kuma batun sayo jiragen ya haifar da zargin Shugaba Muhammadu Buhari ya kwashi kuɗaɗe ya miƙa wa Amurka ba tare da ya sanar wa Majalisar Dattawa ba.
Babban Hafsan Sojojin Saman Najeriya dai ya ce tilas sai an haɗa da hare-haren sojojin ƙasa da kuma Super Tucano ɗin sannan za a iya kakkaɓe matsalar tsaro a ƙasar nan.
Ya ce shugabannin sojojin sama da na ƙasa da na ruwa su na aiki tare domin kawo ƙarshen wannan matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan.
“Tabbas an gurgunta ƙarfin ‘yan bindiga sosai ta hanyar amfani da jiragen yaƙi na Super Tucano A-29.
“Ina tabbatar maku yanzu haka ana kai hare-hare kan ‘yan ta’adda da waɗannan jirage a Arewa maso Gabas.
“Kuma na yi magana da kwamandoji sun tabbatar min ana samun nasara sosai.
“Amma fa ƙarin hasken da na ke son yi a nan, shi ne ba a iya kakkaɓe waɗannan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ta hanyar amfani da jiragen yaƙi samfurin Super Tucano A-29 kaɗai. Tilas sai an riƙa kai masu farmaki ta hanyar amfani da sojojin ƙasa..
“Don ana ganin ana samun nasara ta hanyar amfani da Super Tucano, to kada zauna a dararrashe ana tunanin za a iya galaba kan wannan yaƙi ta hanyar amfani da jiragen yaƙin Super Tucano kaɗai. Sai an haɗa da sauran zaratan jami’an tsaro na fannoni daban-daban.” Inji Amao.
Discussion about this post