Gwamnatin kasar UK tare da hadin gwiwar asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya UNICEF sun samar wa yara 12,043 tsaftace ruwa da muhalli a sansanonin ‘yan gudun hijira 11 dake jihar Barno.
Shugaban sashen hulda da jama’a na UNICEF Ms Folashade Adebayo ta sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labaraia cikin makon jiya.
Folashade ta ce gwamnatin kasar UK da UNICEF sun tallafawa wadannan yara a karkashin shirin ‘Cash4Wash Initiative’.
Cash4Wash Initiative shiri ne da gwamnatin kasar UK ta tsara domin samar da kudaden don taimaka wajen samar da tsaftataccen ruwa da muhalli don yara kanana.
“Rashin tsaftataccen ruwan sha da muhalli na haddasa cututtuka kamar su amai da gudawa dake kisan yara kanana.
Discussion about this post