Gwamnatin Najeriya za ta ciwo bashin Naira tiriliyan 5.012 domin cike giɓin kasafin ƙuɗi na 2022.
Hakan na nufin ana tafiyar ci gaban mai ginin rijiya, ya na dannawa ƙasa, shi kuma ya na cewa gaba ya ke yi.
Yayin da gwamnatin tarayya ke cewa har yanzu bashin da ta ke ciwowa ba mai kumbura ciki ba ne, a gefe ɗaya kuma kuɗaɗen shiga da suka haɗa da ribar mai da haraji mafi yawa su na tafiya ne wajen bashin da ake riƙa biya a hankali duk ƙarshen wata.
A ranar Laraba Majalisar Zartaswa ta amince da kasafin 2022 na Naira tiriliyan 16.39. Hakan kuma na nufin an samu giɓi har na naira tiriliyan 6.258 kenan.
A yau Alhamis ce Buhari zai miƙa kasafin ga gamayyar mambobin majalisar tarayya da ta dattawa.
Yayin da gwamnatin tarayya ke tunanin tara Naira tiriliyan 10.13 a cikin kasafin 2022, sauran giɓin sama da Naira tiriliyan 6 kuma bashi za a ciwo.
Sannan kuma a cikin Naira tiriliyan 10.13 ɗin da za a tara, yawancin kuɗaɗen wajen biyan bashi akai-akai za su riƙa tafiya.
Farkon makon nan PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Bankin Duniya ya ɗirka wa Najeriya bashin dala miliyan 400, domin gaggauta aikin ɗirka wa jama’a rigakafin korona.
Yayin da ake kukan cewa cutar korona ta haifar da ƙuncin rayuwa da karantar tattalin arziki, a gefe ɗaya kuma Bankin Duniya (World Bank) ya amince a a bai wa Najeriya lamunin dala miliyan 400, domin sayen riga-kafin allurar korona.
A ranar Juma’a ce Bankin Duniya ya sanar cewa Daraktocin bankin sun amince a ƙara ɗirka wa Najeriya bashin, baya ga wanda aka bai wa ƙasar a ƙungiyar IDA ta Bankin Duniya.
Yayin da Bankin Duniya ya fitar da sanarwar a birnin Washington na Amurka, ya ce an amince za a bayar da kuɗaɗen ne domin a yi aikin samar da rigakafin korona da kuma gagarimin aikin yi wa ‘yan Najeriya rigakafin mai inganci, kuma a cikin nasara.
Wannan shiri dai ana buƙatar yi wa aƙalla ‘yan Najeriya miliyan 40 rigakafin korona kuma ganin an tallafa wajen ganin aƙalla mutum miliyan 110 sun samu dama ko sauƙin yin rigakafin.
Daga cikin bashin har yau za a yi amfani da wasu kuɗaɗen domin yi shiri da kimtsin bijiro da hanyoyin kaucewa ko shawo kan duk wata barazana da za ta iya fuskantar fannin kiwon lafiya nan gaba.
“Wannan lamuni zai bai wa Najeriya hoɓɓasar ganin aƙalla an yi da kuɗaɗen an wajen yi wa kashi 50 bisa 100 na ‘yan Najeriya rigakafin korona, nan da shekaru biyu.”
Daraktan Bankin Duniya mai Kula da Najeriya, Shulbham Chsudhuri, ya ce yayin da Najeriya ke ta ƙoƙarin daƙile korona zango ta uku, to kuma akwai matuƙar buƙatar an ƙara yi wa jama’a da dama rigakafin korona a faɗin ƙasar.