Wani matashi mai suna Aliyu Na Idris dake zama a cikin birnin Kano da ya rataya wa kansa kwali mai dauke da cewa ganinan na siyarwa ne, ya bayyana cewa tsananin talauci ne ya sa ya ke so ya siyar da kan sa.
BBC Hausa ta ruwaito cewa tuni jami’an Hisbah a Kano suka kama shi domin gudanar da bincike akan sa.
Aliyu Idris mai shekaru 26 kuma tela, ya faɗa cikin matsalar kuɗi, don haka ne ya yanke shawarar sanya farashin naira miliyan 20.
Aliyu ya ce duk wanda ya siyesa zai yi masa hidima tsakanin sa da Allah babu ragwanci.
Sai dai kuma Hukumar Hisbah ta Kano ta kama Aliyu.
Kwamandan Hisba Haruna Ibn Sina ya tabbatar wa da BBC kama Aliyu, yana mai cewa abin da matashin ya aikata ya saba wa karantarwar addini, kuma haramun ne.
”E mun kama shi ranar Talata kuma ya kwana a hannunmu saboda abin da ya akaita haramun ne a addinin Musulinci, ba ka da damar sayar da kanka a kowanne hali ka tsinci kanka” in ji kwamandan.
Aliyu ya yanke shawarar sanya farashin naira miliyan 20.
Kafin kama shi, Aliyu ya faɗa wa ‘yan jarida a Kano cewa: ”Na yanke shawarar sayar da kaina ne saboda talauci, idan na samu mai saye na shirya bai wa iyayena naira miliyan 10, na biya naira miliyan biyar a matsayin haraji ga gwamnati, naira miliyan biyu ga duk wanda ya taimake ni na samu mai saye na, sai na ajiye sauran don amfanin yau da kullum.”