Wata ƙungiya mai bin-diddigin yadda ake gudanar da ayyukan mazaɓu daga kasafin gwamnatin tarayya, ta fallasa wani binciken ƙwaƙwaf da ta yi, tsakanin jihar Ondo da kuma Gundumar Ƙananan Hukumomin FCT Abuja.
Ta bi diddigin ayyukan da aka ware kuɗaɗe aka ce an yi a cikin kasafin 2019 da na 2020.
Rahoton wanda aka raɗa wa suna “Follow the Projects”, ƙungiyar sa-ido ta Technocrat Media Nigeria ce ta gudanar da shi a Ondo da FCT kwanan nan.
Ƙungiyar ta ce an ware naira biliyan 3.905 domin gudanar da ayyukan raya mazaɓu a yankuna 86 a shiyyar Ɗan Majalisar Tarayya 9 cikin yankin Sanatoci uku na jihar Ondo.
“Amma ayyuka 30 kaɗai ƙungiyar mu ta iya ganowa. Cikin 30 ɗin ma akwai waɗanda an watsar da su, ba a kammala ba.
“Sauran 56 kuwa an rasa inda su ke ko inda aka yi su.
“A yankin FCT Abuja kuwa an ware Naira biliyan 1.245 domin a yi ayyuka 17. Sai dai kuma Daraktan ƙungiyar mai suna Dakta Daisi Omokingbe, ya ce aiki ɗaya tal su ka iya ganowa an kammala. Sauran 16 babu wanda ya san inda aka yi su ko kuma yadda aka yi da maƙudan kuɗaɗen da aka ware domin a yi wa talakawa ayyukan.
Daisi ya yi wannan bayani ne yayin taron manema labarai a Abuja, inda ya fallasa masu binciken da ya bankaɗo.