‘Yan bindiga da ke karamar hukumar Sabon Birni sun aika wa hakimin burkusum wasika ya aika zuwa ga iyalan wasu da suka sace cewa su tara kudi su aiko musu don su saki wadanda ke tsare wurin su.
A wasikar da maharan sun nemi sarkin ya aika gidajen wadanda suka sace a kauyukan Gatawa da Burkussum kwanaki biyu da suka wuce, su hada naira miliyan 20 a kawo musu.
Daya daga cikin mutum 20 da suka sace ne aka ba wasikar ya kawa wa sarkin.
” Yan bindigan sun baiwa daya daga cikin wadanda suka sace ya kawo wa sarkin wasikar. Sun ce saboda rashin waya da za su yi kira da shi dole suka saki mutum daya su hakura dashi domin su isar da sakon su.
Discussion about this post