Gargaɗi: Wannan Nazari Na Musamman haƙƙin mallakar PREMIUM TIMES ne, don haka masu karatu su kiyaye. Inda duk aka ga wannan nazari, to daga shafin mu aka ɗauke shi ba da iznin mu ba. A sha karatu lafiya.
Duk da a yanzu farashin ɗanyen mai duk ganga ɗaya ya doshi dala 100 a kasuwar duniya, wannan ƙarin farashi da za a ce ya nunka cikin ƙanƙanen lokaci, ba abin alheri ba ne ga tattalin arzikin Najeriya.
Domin matsawar Najeriya za ta riƙa kashe kuɗaɗen cikinin ɗanyen fetur da ta yi a duniya ta na sayo tataccen fetur da gas da man jiragen sama duk daga ƙasashen Turai, to maƙudan kuɗaɗen cinikin ɗanyen man fetur sun tafi a banza kenan, ba za su yi wani tasiri ga bunƙasa tattalin arzikin Najeriya ba.
Najeriya ta yi Kasafin 2022 na Naira tiriliyan 16.39, amma kuma kuɗaɗen shigar da za ta samu a shekarar, ba su kai Naira tiriliyan 11 ba.
Wato kenan sai an ciwo bashin Naira tiriliyan sama da 5 domin a cike giɓin da ke cikin kasafin na 2022.
An rattaba wannan kasafi ne a kan za a riƙa sayar da gangar ɗanyen mai ɗaya a kan dala 57.
Najeriya ta yi kasafin ne a bisa maleji da ma’aunin ƙarfin yawan gangar ɗanyen mai miliyan 1.8 da Ƙungiyar OPEC ts Duniya ta amince ta riƙa haƙowa a kullum.
Ya kamata a ce yawan ɗanyen man da Najeriya za ta riƙa haƙowa a kullum ya bunƙasa tattalin arzikin ƙasar, musamman yin la’akari da cewa farashin kowace ganga a duniya ya doshi dala 100. To sai dai abin ba haka ya ke ba a Najeriya.
Najeriya: Ƙasaitacciyar Ƙasa Mai Girman Kwabo:
Yawan gangar ɗanyen mai har miliyan 1 da 800,000 da OPEC ta amince Najeriya ta riƙa haƙowa, hanya ce ta samu maƙudan biliyoyin daloli. To amma kuma ‘garin banza, wai a farau-farau ɗin banza ya ke ƙarewa’.
Dalili, dukkan matatun mai huɗu na Najeriya da ke Kaduna, Warri, Lagos da Fatakwal sun shafe shekaru ba su iya tace ko fetur cikin garwar shayi.
Tilas duk wani fetur da masu mota, babur, janareto za su sha a kullum a ƙasar nan, sai Najeriya ta yi amfani da dalolin da ta sayar da ɗanyen mai za ta sayo.
Haka kuma da dalolin za ta yi amfani ta sayo gas, man jiragen sama da sauran nau’ukan man da ake buƙata.
A yanzu haka Najeriya ba ta ma iya haƙo ganga miliyan 1.8 da OPEC ta amince ta riƙa haƙowa a kullum.
Cikin watan Agusta an riƙa haƙo ganga miliyan 1.2 kacal. A cikin Yuli kuwa ganga miliyan 1.3 aka riƙa haƙowa.
Manyan ƙasashen duniya da su ka fi amfani ko sayen ɗanyen mai, irin su Indiya da Amerika, sai da amincewar su farashi da yawan ɗanyen mai da ake sayarwa a duniya ke daidaita.
Waɗannan ƙasashe biyu na so a ƙara wa ƙasashe masu arzikin fetur damar ƙara haƙo gangar mai, ta yadda farashin sa a kasuwa ba zai riƙa yin tashin-gwauron-zabo ba.
Yadda Matatar Mai Ta Ɗangote Za Ta Ceci Najeriya – Emefiele, Gwamnan CBN:
Kwanan nan Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN ya bayyana cewa hanya ɗaya tak da Najeriya za ta dogara da ita, shi ne ta ga an gaggauta kammala Matatar Mai ta Ɗangote da ke sa ran kammala ginin ta cikin 2022 a Lagos.
“Idan aka kammala ginin wannan matata, za ta riƙa tace ganga 650,000 a kullum.
“To mu na sa ran ko da ganga 450,000 mu ka riƙa saye a hannun Ɗangote Refinery ai da naira za mu riƙa biyan sa. Shi kuma ya saida sauran a waje da dala.
“To kun ga haka zai magance wa Najeriya kwasar kashi 40 bisa 100 na dalolin da ta ke samu a cinikin gangar ɗanyen mai a duniya, ta na sayo tataccen fetur da su.
“Sannan kuma a hada-hadar sayo tataccen fetur daga waje, akwai kashe kuɗaɗe masu yawa bayan farashin sa na ainihi. Ga kuɗin lodi a manyan tankunan jiragen ruwa daga waje. Ka kuɗin tsaron sa daga cikin teku har zuwa Najeriya. Ga kuɗin saukale idan an zo nan tashoshin ruwan mu.”
Emefiele ya ƙara da cewa, “to kun ga kenan idan mu na samun tataccen fetur a Matatar Dangote mu na saye a nan gida, mun huta da kashe daloli a waje. Shi da naira za mu biya wani yardajjen adadin yawan mai a hannun sa. Kuma mun huta da kashe kuɗaɗe wajen ɗawainiya da jeƙala-jeƙalar shigo da tataccen fetur da sauran nau’ukan mai daga Turai.”
Ita kuwa Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed Ahmed, cewa ta yi “ƙarin farashin gangar ɗanyen mai a duniya, ba ƙarin kuɗin shiga ba ne ga Najeriya. Saboda hidimomin kashe kuɗaɗe sun yi wa gwamnati yawa ƙwarai da gaske.
A cewar ta, gejin gangar ɗanyen mai a shekarar nan ta 2021, ya na kan hasashen dala 40 ne duk ganga ɗaya.
Amma kuma duk da an yi kasafin 2022 a kan hasashen ganga ɗaya dala 57, yanzu har ta kai dala 85, tun ma ba a shiga 2022 ɗin ba.
“Sai dai kuma wannan duk lissafin-dawakan-Rano ne”, inji Gwamnan CBN Emefiele.
“Gatan Najeriya da gadarar ta kawai shi ne Masana’antar Tatar Ɗanyen Mai ta Ɗangote.”
Duniya mai abin mamaki. Allah gatan bawa. Ɗangote gatan Najeriya. Ɗangote ya zama ɗuwawun Najeriya, tilas a zauna a kan sa, ko a yini a tsaye!
Discussion about this post