Gwamnan jihar Ondo rotimi Akeredolu ya bayyana cewa Najeriya ta wuce zamanin a rika bari ana gararambar kiwon dabbobi a ko ina kamar yadda ake yi shine ya sa gwamnonin yankin Kudu Maso Yamma suka hana da karfin tsiya.
Wannan yana kunshe ne a jawabin da gwamnan yayi a wajen taron Bunkasa tattalin Arziki da ake yi a Abuja.
” Makiyaya sun zama annoba a yankin mu. In banda tashin hankali da suke yi jawo mana da rashin kwanciyan hankali tsakanin mutanen yankin mu babu abinda kiwo ya ke kawo mana.
” Manoma da makiyaya ba su jituwa saboda ayyukan makiyayan. Sannan kuma abin haushi shine kauda fuskar da ‘yan sanda suka yi. Ba su kama makiyayan masu laifi. Sai su yi barbar su su yi tafiyar su ba tare da sun hukunta su ba.
” Wanna shine dalilin da ya sa na muka kirkiro da rundunar Amotekun. Yanzu babu wani makiyayin da ya isa ya gitta ta yankin jihohin mu, idan ko ya yi taurin kai zai kuka da kan sa domin Amotekun na jiran sa.
Sai dai kuma gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi hannun riga da wannan ra’ayi na gwamna Akeredolu in da ya ce wannan matsaya na gwamnonin Kudu siyaysa ce kawai.
” Ban ga dalilin da za a ce wai an hana kiwo ba, za a iya kakkafa wa makiyaya wuraren kiwo da rugage, duk duniya haka akeyi kuma a kasar nan muna da isasshen kasa da za mu iyay yi wa ,makiyaya haka.