Babbar Kotun Jihar Neja da ke Minna, ta umarci sabon Sarkin Kontagora ya daina kiran kan sa Sarkin Sudan na Kwantagora na 17.
Kotun ta bayar da wannan umarni bayan da sauran gamayyar ‘yan takara su 15 su ka shigar da ƙarar Muhammad Barau wanda aka naɗa.
Tare da sabon Sarkin, an kuma maka Kwamishinan Harkokin Ƙananan da Masarautu na Jihar Neja a kotu.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Gwamna Abubakar Bello na Jihar Neja ya soke naɗin da ya yi wa sarkin, bayan sauran masu takara su 46 sun rubuta takardu na ƙorafin cewa an yi maguɗi wurin zaɓen sabon sarkin.
Bayan kwanaki kaɗan kuma sai Gwamnati ta bayyana sunan Barau a matsayin sabon Sarkin Kwantagora.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta maida sunan Mohammed Barau ne bayan ta bincika kuma tabbatar cewa tsarin zaɓen na sa da aka soke, a kan ƙa’idar cancanta aka zaɓe shi.
Sai dai kuma a ranar Talata Mai Shari’a Abdullahi Mikailu ya dakatar da Barau daga kiran kan sa Sarkin Sudan na Kwantagora, na 7 har sai kotu ta kammala sauraren ƙarar da masu ƙorafin su ka kai mata tukunna, wanda su ka shigar a ranar 11 Ga Oktoba, 2021.
“Babbar Kotu ta umarci wanda ake ƙara ya daina kiran kan sa Sarkin Sudan na Kwantagora na 7 tukunna, har sai an ga yadda shari’ar ƙarar sa a ake yi ta kaya tukunna. An shigar da ƙarar sa a ranar 11 Ga Oktoba, 2021.”
Lauyan masu ƙara W.Y Mamman Esq ne ya roƙi kotu ta hana sarkin kiran kan sa Sarkin Kwantagora.
Za a ci gaba da shari’a a ranar 20 Ga Oktoba.