Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo ya ragargaji Majalisar Dattawa, saboda maƙala wata saɗarar a cikin Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe, inda su ka amince tilas jam’iyyun siyasa su yi tsarin zaɓen-kai-tsaye wajen fitar da ‘yan takara, a lokacin zaɓen fidda-gwani.
Lamiɗo wanda jigo ne a cikin jam’iyyar PDP, kuma wanda da shi aka kafa jam’iyyar, sannan bai taɓa ficewa a cikin ta ya sauya sheƙa ba, ya bayyana cewa ƙunshin saɗarar da Majalisar Dattawa ta cusa s cikin ƙudirin gyaran dokokin zaɓen su kauce wa Dokar Najeriya kwata-kwata.
Daga nan sai ya yi kira ga jam’iyyar PDP kada ta amince da wannan ƙudiri, ta yi gaggawar garzayawa kotu kawai, domin a hana ƙudirin zama doka.
A ranar Talata ce Majalisar Dattawa ta shigar da saɗarar, bayan ta sake nazarin matsayar da ta ɗauka a baya, ta yadda ta yi daidaito da na Majalisar Tarayya a kan tsayar da ‘yan takara a jam’iyyun siyasa.
Yayin da Shugaban Kwamitin Zaɓe na Majalisar Dattawa, Sanata Kabiru Gaya, ya kare ƙudirin da su ka cusa ɗin, inda ya ce dokar za ta kawo karshen kaka-gidan da gwamnoni ke yi a cikin jam’iyyar su.
Amma shi Sule Lamiɗo bai goyi bayan sa ba. Cewa ya yi “dokar Najeriya ta bai wa jam’iyyun siyasa damar gudanar da sha’anin zaɓen fidda gwani kamar yadda doka ta tanadar a bisa sa-idon Hukumar Zaɓe.
“Amma a yanzu Majalisar Dattawa wadda APC ce ke juya akalar ta yadda ta ga dama, ƙiriƙiri ta zama wata kantomar kula da jam’iyyun siyasa.”
Lamiɗo ya buga misali da irin yadda aka naɗa wa jam’iyyu kantoma a lokacin NRC da SDP a zamanin sojoji, kuma gwamnati ce ke ɗaukar komai na ofishin jam’iyya a lokacin.
Yayin da zaɓen kai-tsaye na nufin duk wani ɗan jam’iyya ya shiga zaɓen fidda ɗan takara, shi kuma zaɓen ‘yar gida na nufin wakilan shugabannin jam’iyya tun daga mazaɓu zuwa sama ne za su yi zaɓen fidda ɗan takara.
A baya dai an sha ƙorafin cewa gwamnoni ne ke murɗe zaɓen, ta hanyar juya akalar wakilai masu zaɓe yadda su ke so.