Gwamnatin Jihar Kano ta umarci cewa tilas duk wani ɗan takarar da ke neman kowane muƙami a shugabancin APC ta Jihar Kano, sai an yi masa gwaji domin a gano ya na tu’ammali da muggan ƙwayoyi ko ba ya yi.
Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba ya sa wa hannu, kuma ya fitar a safiyar Laraba ɗin nan.
Garba ya ce duk mai sha’awar tsayawa takara to ya fara garzayawa Ofishin Hukumar Hana Sha da Fataucin Muggan Ƙwayoyi (NDLEA), domin a tantance shi kafin ƙarfe 7 na safe.
“Wannan umarni ya na daga cikin namijin ƙoƙarin da Gwamnatin Jihar Kano ke yi domin kakkaɓe jihar daga masu tu’ammali da muggan ƙwayoyi.” Inji sanarwar.
Ya ce babu wani ɗan takarar da za a tantance har sai ya gabatar da katin shaidar shi ba ɗan ƙwaya ba ne.
Za a gudanar da taron gangamin yin zaɓen a ranar 16 Ga Oktoba, 2021.
“An yi wa ‘yan takarar zaɓen shugabancin ƙananan hukumomi da masu riƙe da muƙaman siyasa da gwamna ya naɗa. Kuma su ma kwamishinonin da aka naɗa sai da aka yi masu irin wannan gwani.” Cewar Garba.
Ya ƙara da cewa tuni Gwamna Ganduje ya umarci jami’an NDLEA su yi ɗawainiyar yi wa ‘yan takarar gwaji.
Idan ba a manta ba, ranar 8 Ga Janairu an soke ‘yan takarar kansila su 13, saboda gwaji ya nuna cewa su na shan muggan ƙwayoyi.