Idan aka auna da sikeli GDP, za a iya cewa a farkon shekarun 1980s ne Najeriya ta fi samun kan ta a koma-bayan ƙarfin tattalin arzikin cikin ƙasa. A wancan lokacin kuwa lamarin ya shafi duniya ce baki ɗaya, ba Najeriya kaɗai ba.
Ana cikin wannan mawuyacin hali ne a ƙarƙashin mulkin dimokraɗiyya na Shehu Shagari, sai sojoji su ka yi juyin mulki, Manjo Janar (ritaya) Muhammadu Buhari ya hau mulki, ranar 31 Ga Disamba, 1983.
Mene Ne GDP?: A fassara game-gari dai GDP na nufin yawan adadin darajar kuɗaɗen da jama’a su ka sayi kaya, yawan kuɗaɗen da ‘yan kasuwa su ka kashe da yawan waɗanda gwamnati ta kashe.
Za kuma a iya fassarawa da darajar dukkan kayayyaki da ayyukan da aka yi a cikin ƙasa a cikin wani ƙayyadajjen lokaci.
GDP: Ba Girin-girin Ba, Ta Yi Mai: An fi auna sassaucin rayuwa ko shiga ƙuncin rayuwa da adadin kuɗaɗen da ke shiga hannun jama’a, tare da yin la’akari da abin da ƙarfin aljihun su ke iya saye.
Duk da cewa an hamɓaras da mulkin soja na Muhammadu Buhari, za a iya gamsuwa da cewa a zamanin mulkin sa ne na tsawon watanni 20 GDP ɗin ƙarfin arzikin cikin gidan Najeriya ya fi haɓaka. Haka dai Bankin Duniya ya bayyana a cikin rahoton sa na baya-bayan nan.
Mulkin Buhari Na Soja: An Gyara Ƙasa, An Jefa ‘Yan Ƙasa Cikin Garari:
A lokacin da Buhari ya karɓi mulki ƙarshen Disamba, 1983, ƙarfin tattalin arzikin cikin gida na -10.92%. Amma kafin ya sauka, sai da ƙarfin wato GDP ya kai 5.92%. Kenan ya ƙaru da kashi 16.83.
Sai dai kuma hawan sa ke da wuya farashin kayan abinci da na masarufi su ka yi tsananin tsada.
Wasu tsare-tsaren inganta arziki da Buhari ya shigo da su, kamar canjin kuɗi, ya jefa ‘yan ƙasa cikin garari matuƙa.
Daga nan tattalin arzikin cikin gida bai bunƙasa ba sai ɗan taƙitaccen watannin da Murtala Mohammed ya yi na watanni bakwai a kan mulki.
A lokacin da aka kashe Murtala a yunƙurin juyin mulki, ƙarfin tattalin arzikin Najeriya na da 9.04% ne.
Shi kuma Murtala ya yi wa Yakubu Gowon juyin mulki a lokacin da ƙarfin tattalin arzikin cikin gida na Najeriya ke -5.23%.
Murtala ya ƙara shi da kashi 14.27 kenan.
Mulkin Gowon: Ga Yaƙin Basasa Ga Ƙarin Albashi: Yakubu Gowon a farkon mulkin sa ya fuskanci gagarimar rigimar yaƙin Basasa tsawon watanni 30. Amma wannan bai hana shi yi wa ma’aikatan gwamnati a Najeriya garaɓasar ƙarin albashin lokaci guda ba.
A lokacin da aka yi bada kuɗaɗen bayan kwamitin Udoji ya amince a yi ƙarin, malamin makaranta mai karɓar albashin Naira 60 a wata, an damƙa masa fam 200, wato Naira 400 kenan (ko a ce jaka 2).
Lokacin da Olusegun Obasanjo ya sauka daga mulkin soja cikin 1979, ƙarfin tattalin arzikin, cikin gidan Najeriya ya koma baya zuwa 6.59.
A shekaru 8 da Obasanjo ya sake yi a matsayin shugaban mulkin farar-hula, daga 1999 zuwa 2007, ƙarfin GDP ya yi sama daga 0.58 zuwa 6.59.
Ita kuwa Jamhuriya ta Farko a karkashin Firayi Minista Tafawa Ɓalewa, an ɗan samu ƙarin GDP daga
1.89 a 1960 zuwa 4.89% a 1965.
Lokacin da Sani Abacha ya karɓe mulki daga hannun gwamnatin riƙon ƙwarya ta Eanest Shonekan, cikin 1993, ya samu tattalin arziki na -1.81%. Kafin ya mutu ya kai shi kashi 2.58%.
Wato an samu ƙarin kashi 4.39 kenan a lokacin Abacha.
Gwamnatin Abacha ta tara kuɗin fetur har dala biliyan 64 a tsakanin 1993 zuwa 1998 a ƙarshen mulkin sa. Haka dai Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arzikin Fetur (OPEC) ta wallafa.
Gwamnatin Abacha ta ƙara yawan kuɗaɗen asusun Najeriya na ƙasashen waje, daga Dala miliyan 494 a 1993 zuwa dala biliyan 9.6 a tsakiyar 1997.
Sannan kuma Abacha ya rage yawan bashin da ake bin Najeriya daga dala biliyan 36 zuwa dala biliyan 27 a tsakanin 1993 zuwa 1997.”
Umaru ‘Yar’Adua ya yi shakaru uku daga 2007 zuwa 2010. Shi ya gaji Obasanjo, kuma tattalin arzikin cikin gida Najeriya ya ƙaru daga 6.59 zuwa 8.01.
An samu ribar fetur har dala biliyan 261.8 a ƙarƙashin gwamnatin Obasanjo, a lokacin Umaru kuwa an samu dala biliyan 139. Kamar yadda OPEC ta fitar da rahoto.
Gwamnatin Goodluck Jonathan ce ta fi saura samun ribar fetur, har dala biliyan 381.9. Sai dai kuma ya samu GDP ta kai 8.01, amma ya bar shi a kashi 2.65%.
Lokacin da Shonekan ya hau, ya gaji GDP na -2.04 daga Ibrahim Babangida, ya bar ta a -1.81. Amma yayin da Abacha ya hamɓarar da shi, ta na 0.23%.
Wato dai a lokacin Gowon ne Najeriya ta fi samun ƙarfin GDP, bayan an gama Yaƙin Basasa, wanda ya kashe miliyoyin mutane.
Buhari ya gaji GDP ta na 2.65, kuma zuwa yanzu raguwa ya yi ba ƙaruwa ba zuwa 2.21%. Wannan kuwa matsalar faɗuwar farashin ɗanyen mai ne da kuma ɓarkewar cutar korona.
Lokacin Aguiyi Ironsi GDP raguwa ya yi zuwa -4.3. Haka lokacin Shagari zuwa -6.7.
Ƙarfin Nauyin Aljihun ‘Yan Najeriya Daga Samun ‘Yanci Zuwa Yau:
A lokacin mulkin Jonathan ne aka fi samun ƙarfin nauyin aljihun ‘yan Najeriya ya kai dala 2,792.
Lokacin Umaru dala 2,138, a yanzu lokacin Buhari, ƙarfin nauyin aljihun ‘yan Najeriya ya na dala 2,097 idan aka auna yawan al’ummar ƙasar a sikelin yawan ƙarfin tattalin arzikin ta.