Ƴan fashin daji da suka kama Sarkin Ɓungudu, dake Jihar Zamfara, Hassan Attahiru, sun karɓi kuɗi fiye da naira miliyan 20 kafin sakin Sarkin bayan ya shafe kwanaki 32 a daji.
Ƴan Bindigar sun tare tawagar Sarki ne a Jihar Kaduna cikin watan jiya akan hayarsa ta zuwa Abuja. An sace shi sati biyu kafin a yanke kafofin sadarwa ta waya a wasu bangare na Jihar Kaduna.
Yanke kafafen sadarwar a Kaduna da wasu Jahohin Arewa na daya daga cikin matakan da gwamnonin yankin suka ɗauka domin magance ayyukan ƴan bindiga da suka addabi jihohin.
Toshe kafar sadarwar a Kaduna ya kawo cikas wajen jinkirin magana da ƴan Bindigan ta waya domin kawo kudin fansar.
Wane Basarake daga masarautar ta Bunguda wanda bai so a bayyana sunansa ba yace sai da aka fara biyan naira miliyan N20 kafin a yanke kafar sadarwar.
Dalilin toshe kafafen sadarwar, Ƴan Bindigan sun riƙa faɗi-tashi wajen neman sabis, da suka samu sai suka bukaci a kara musu naira miliyan 100 bayan miliyan N20 da aka basu da farko.
Wanda ya kai naira miliyan N20 na farko ya tafi cikin dajin ne akan babur daga garin Rigachikum, jihar Kaduna inda yayi tafiya har na kusan awa uku, amma duk da haka daya ji bai sami ganinsu sai ya dawo da kudin garin Kaduna.
Amma yana shigowa gari sai Ƴan Bindigan suka kuma kira sa suka ce masa ya dawo cikin daji ya kawo kuɗin, haka ya buga babur ya sake nunƙayawa cikin dajin ya basu wannan kuɗi cike maƙil a jakar buhu wato bako.
Duk da haka Ƴan Bindiga sun ki su sake Sarkin sai da aka kara musu wasu miliyoyin nairori kafin suka sake shi.
.