Rundunar ‘yan sandan jihar Barno ta gabatar da wasu batagari 76 da ta kama a cikin wata daya a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Abdu Umar ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a garin Maiduguri.
Umar ya kara da cewa wadanda aka kama sun aikata laifuka kamar haka, kisa, fashi da makami, garkuwa da mutane, fyade, yawo da makamai da dai sauran su.
“Ina mai tabbatar wa ‘yan jihar Barno cewa za mu ci gaba da amfani da fasaha domin kare rayuka da dukiyoyin mutane masu kiyaye dokar ƙasa sannan kuma za mu rika farautar batagari irin wadannan domin hukunta su.
Umar ya yi kira ga mutane da su rika taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri domin samun nasarar kama yan iskan gari.
Discussion about this post