Ita fa Dimokaradiyya tazo ne don kawar da mulkin danniya da babakere da wasu mutane kalilan kanyi akn sauran al’umma.
Dimokaradiyya ce kadai da take bawa al’ummah damar yiwa kansu shugabanci da jagoranci ta hanyar sahihin zabe daga matakin primary na jama’iyyu zuwa zaben gama-gari.
Jam’iyyun siyasa gangami ne na mutane masu ra’ayi iri daya da manufa iri daya da suka aminta da ita a kan mafita wajen ciyar da kasa da al’ummar gaba.
Jama’iyya a siyasance kan bawa duk wani danta dama da yanci sa, a kan ra’ayin wanda zai jagorance shi a siyasan ce, koma ya tsaya masa takara a kowa ne bigere, amma sabanin haka zai iya zama wani abu da ban ba jama’iyya ba.
Akan iya alakanta koma bayan dimokaradiyyar Nigeria bisa la’akari da yadda, manyan jama’iyun kasar nan suka kasa zama da gindinsu, suka kasa bayyana manufofinsu da alkibilar su. A yau jagororin siyasar kasar nan, an gaza fahimtar ra’ayoyin su, tunda kullum suna tsalle ne tsakanin wannan jama’iyyu da zarar burin su bai cika ba a cikin tafiyar.
A yanzu an doshi kakar zabe mai zuwa ta badi, duka hankalin shugabbanni ya koma yaya za kafa gwamnati a shekarar 2023, ba tare da yin tunanin shin an sauke nauyin alkawuran da aka dauka a baya ba.
A kokarin wadannan jama’iyyu manya na APC da PDP da zabar shugaban nin jama’iyya, kowa zai iya gannin yadda kokuwar mallake jama’iyun nan da yin kama-karya na manyan ‘yan sisayasa da masu rike da iko ya fito fili.
A zaben shugabbannin jama’iyar APC kadai jahohi tara sun yi zabe kasha biyu-biyu kamar jahar Kano, Enugu, Osun, Bauchi, Kwara da Niger.
A Kano Abdullahi Abbas wanda yake da goyon bayan Gwamnan Kana Dr. Umar Ganduje an zabe shi a matsayin shugaba, a wani bangaran kuma bisa jagorancin Senator Ibrahim Shekarau kuma tsohon gwamnan Kanon sun zabi Alhaji Danzago a matsayin shugaba.
Haka zalika a Jahar Osun bangaren Ministan Cikin Gida Rauf Aribisola kuma tsohon gwamnan sun zabi Mr. Prince Gboyega a matsayin shugaba sannan bangaren shugaban jama’iyar ya zabi Mr. Rasaq Salinsile a matsayin shugaba.
A jahar Akwa Ibom kuwa har zabe kala uku aka yi. Bangaren Ministan Niger Delta Senator Godswill Akpabio yayi nasa daban, wanda Mr. Ntukepo ya zama shugaba. A daya hannun kuma mai rikon Jama’iyar APC na Jahar, wanda yake goyon bayan Senator John Akpanudoehe sun fitar da Mr. Agustine Ekanem a matsayin shugaba.
Su kuma bangaren Babban Mataimakawa Shugaba Buhari (SSA to the President on Niger Delta) Senator Ita Enang ta zabi Mr. Douglas Pepple a matsayin shugaba.
Ita ma kanta babbar Jama’iyar adawa ta PDP akwai irin wadannan rigingimun masu kama da juna, kamar yadda aka ga rigimar yayin fidda shugabannin jama’iyar PDP na shiyar Arewa-maso-Yamma tsakanin bangaren Senator Rabi Musa Kwankwaso da bangaren Gwmna Aminu Waziri Tambuwal na Sakkoto. Haka zalika a shiyar Kudu-maso-Yamma tsakanin shugaban PDP na yankin da Gwamnan jahar Oyo, Engr. Seyi Makinde suna galubalantar Sam Anyawu a matsayin mai tsawa Sakataren Jama’iyyar na Kasa.
A yanzu ma tsohon shugaban jama’iyyar PDP wato Uche Secondus ya gurfanar da jama’iyar a gaban Alkali duk da cewa a 30 da 31 na watan October na wannan shekarar Jma’iyar zata gudanar da zaben shugaban nin ta.
Idan muka yi tsim da nazari a kan wannan rigingimum, zama muyi tsinkayar cewa duk manyan masu rigimar, sune suke jagorancin kasar, da ga Gwamna sai Tsohon Gwaman, da ga Minister sai Tsohon Minista, daga Sanata sai Tsohon Sanata, sai kuma masu biye musu shugabannin jama’iyya masu ci da wayanda suka sauka.
Sannan za mu iya ganin cewa kowa kokuwa yake don yakai bakin sa, kowa so yake ya kafa nasa ko yaron sa ko kuma makusancin sa a kan mugaman da ake rigima a kansu.
Shin a wannan yanayi ina matsayin dan jama’iyya da ya yanki kati don zama dan jama’iyyar? Ina yancin sa da hakin sa yake na zaben shugaban sa? Shin in ma dimokaradiyyar a aikace?
A zahiri, yanayin yadda a ke tafiyar da jama’iyyu a Nijeriya ya zamo kamar wani sabon salon a mallakar mutane ta ko yaya ta hanyar amfani da dimokaradiyya da cin moriyarta ta wajen tauye wa kowa hakinsa sai kawai masu mulki suyi abin da suka ga dama domin biyan bukatar kansu da son dawwama a madafun iko irin na mulukiyya.
Wannan babkeren ya sanya sama da shekara 20 wadan nan jagororin suka kasa fidda kasar nan daga halin kaito na talauchi, rashin tsaro da tabarbarewar da lafiya da ilimi, uwa uba suna neman rusa kasar ma baki daya.
In har baza a kauda san rai ba, a bawa kowa ne dan jama’iyya damar taka rawar sa a siyasance to fa da kyar kwalliya zata biya kudin sabulu.
Yan mulukiyya sun sa rigar dimokaradiyya don su dinga tabbabata a kan mulki da juya siyasa, wannan ya sanya suka rasa alkibila da jama’iyyar da za zauna a cikinta do ciyar da kasa gaba.
alhajilllah@gmail.com