Sahihan bayanai sun bayyana a kan yadda aka kama Umar Bature, wani tsohon ɗan majalisar tarayyar Najeriya a Landan, ya na watandar kuɗaɗen da ake zargin cewa na Tsohon Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro ne, Janar (mai ritaya) Aliyu Gusau ne.
Bature dai an kama shi ne an kama shi da maƙudan kuɗaɗen da zargin na harƙallar Malabu ne.
Wasu sahihan takardun bayanai da su ka gitta ta gaban PREMIUM TIMES, ta yi wuf ta danne, jaridar ta ga hujjojin da kamfanin mai na Eni ya gabatar a kotun Amurka.
An zargi Tesler wanda Baturen Birtaniya ne da laifin harƙallar Halliburton-Bonny Island da ta shafi bayar da cin hanci ga wasu jami’an gwamnatin Najeriya.
Gusau ya kasance shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta Sojoji tsakanin 1988 da 1989. Daga nan Daraktan Tsaron Ƙasa na tsoffin shugabannin da su ka haɗa da Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan. Kuma ya zama Ministan Tsaro na wani ɗan lokaci a ƙarƙashin gwamantin Jonathan.
Shi kuma yaron sa ko a ce ɗan-koren sa Umar Bature, ya taɓa zama ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Sokoto ta Arewa da Sokoto ta Kudu.
Bature tsohon soja ne da ya yi ritaya cikin 2003, ya shiga siyasa.
An haƙkaƙe cewa yaron ke riƙe wa Aliyu Gusau sitiyarin harkokin hada-hadar sa ne a lokacin da ya ke soja.
A yanzu Bature shi ne Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Sokoto.
PREMIUM TIMES ta fi kowace jaridar Hausa a duniya bin diddigin buga labaran harƙallar Malabu, har ta dala biliyan 1.1, wadda aka yi watandar kuɗaɗen tare da wasu jami’an gwamnati, ta hannun asusun ajiyar Ministan Harkokin Fetur na lokacin, Dan Etete.
Masu gabatar da ƙara sun shaida wa kotu yadda aka kwashi sama da dala miliyan 500 daga asusun Etete, aka tura asusun ɗan gada-gada Aliyu Abubakar, wanda aka fi sani da AA Oil a Abuja.
Masu yaƙi da cin rashawa sun ce AA Oil karen farautar wasu manyan jami’an gwamnatin Jonathan ne da kuma wasu manyan ma’aikatan Shell da Eni. Ya dai musanta zarge-zargen da ake yi masa.
Harƙallar Malabu dai an yi ta ne lokacin gwamnatin Jonathan, cikin 2011, inda aka sayar da lasisin rijiyar mai lamba OPL 245 a arha takyaf.
Rigimar Duniya Da Mai Rai Ake Yi: Yadda Aka Kama Umar Bature Da Maƙudan Daloli A Landan:
A ranar 9 Ga Janairu, 2014, Tesler ya kai kan sa wani ofishin ‘yan sanda a Landan, ɗauke da jakar kuɗi har fam na Ingila 378,670 a ciki, kuma ya damƙa su ga ‘yan sanda. Sannan kuma ya rubuta cewa Umar Bature ya kawo masa kuɗaɗen daga Najeriya.
Shi dai Tesler ya ƙulla yarjejeniyar ba shi rigar kariyar kauce wa hukunci da gwamnatin Amurka, inda ya yarda zai riƙa tsegunta wa hukuma duk wata daƙa-daƙar Malabu. Wato ya zama infoma kenan.
A ranar 15 Ga Nuwamba, 2013 wani ɗan Najeriya mai suna “Umar Bature” ya sanar da shi cewa ya turo asusun banki a wani ofishin ‘yan canji a Abuja, domin a tura masa dala miliyan 2 daga Dan Etete.
Tesler ya ce ba shi da asusun da za a iya tura masa kuɗaɗen ba.
Daga nan sai Umar ya ce to sai dai ya karkasa kuɗin a kai masa a Landan.
“Tesler ya ce a haɗuwar sa ta farko da Bature bai ce masa ga dalilin da ya sa aka ba shi kuɗin ba.”
“Tesler ya kwashe duk abin da ya faru a haɗuwar sa da Umar Bature, ya rubuce tsaf, ya miƙa wa lauyoyin sa, domin sanar da mahukuntan Amurka.”
“Tesler ya shaida wa ‘yan sandan Amurka cewa a ranar 8 Ga Janairu 2014, Aliyu Gusau ya kira shi, ya sanar da shi cewa nan da ‘yan mintina wani zai kira shi.”
“Karfe 7:15 daidai sai na ji kira, wani ya ce min ni ne Umar Bature, wanda ku ka taɓa haɗuwa wata rana. Ya ce ya na so mu haɗu ya ba ni wani abu.”
“Su ka tsayar da lokaci cewa za su haɗu a Cavendish Hotel, da ke kan titin German da ƙarfe 8 na safe, a unguwar Piccadilly.”
Nan da nan Tesler ya sanar da lauyoyin sa. Su ka ce masa kuɗi ne Umar Bature zai ba ka. Ka karɓa, amma kada ka kashe.
“Bayan ya karɓi kuɗi, ya sanar da lauyoyin sa. Su ka ce masa kada ya sake ya bi Bature su fita wani wuri. Kuma wani jami’in tsaron FBI zai kira shi, ya ba shi umarni.
Tesler ya ce daga nan sun riƙa haɗuwa da Umar Bature a Landan, har kamar sau huɗu ko sau shida. Har ya kai masa fam miliyan 200.
Ya tambaye shi kuɗin waɗanda Etete ke aikowa ana ba shi, ko na mene ne. Ya ce ba ya so a jefa shi cikin tsomomuwa.
Da jami’an ‘yan sandan Landan su ka tambaye shi ko ya san kuɗin ko na mene ne, sai Tesler ya ce masu ai waɗannan kaɗan ne, idan aka kwatanta da waɗanda kamfanonin Shell da Agip su ka ba shi.”
Takardun bayanan sun nuna cewa washegarin ranar da Tesler ya kai kuɗi ofishin ‘yan sanda, jami’an Yaƙi Da Shawara na ‘Yan Sandan Scotland Yard na Landan sun damƙe Umar Bature.
An yi masa tambayi ya amsa yadda wani abokin ogan sa ya ba shi dala miliyan 1.4 ya kai wa Tesler.
Tesler ya shaida wa ‘yan sanda cewa a hotel sai Bature ya ɗauko wata jakar kuɗi ya ba shi, kuma ya ce masa washegari ya dawo ya sake ba shi wasu kuɗin. Ya ce fam 378,000 Bature ya ba shi.
PREMIUM TIMES ta kira wayar Aliyu Gusau ba ta same shi ba. An tura masa saƙon tes, har zuwa yau bai maido amsa ba.
Shi kuma Bature an kira shi a jiya Alhamis, sai ya ce shi ba shi da abin da zai ce. Wai uwar gulma ta yi cikin-shege.