Duk da kasancewar akwai abubuwa masu tarun yawa da Nijeriya zata yi alfahari da shi na cigaba a wannan lokacin da kasar ta shekara 61 da samun ‘yanci kai, musamma tsakaninn takwarorinta na Africa.
Nijeriya zatayi alfaharin kasancewar kasa daya a tsawan wannan lokacin, duk da kasan cewar barazana da ta yi ta fuskanta irin na su yakin basasa da aka dauki tsawon shekaru 4 ana yi, kafin a kawo karshen sa a shekara 1970.
A shekarun nan ma Nijeriaya ta sha fama da barazanar ta’addanci da yunkurin kafa daular musulunci a arewa-maso-gabas daga kungiyar Boko Haram da ma yunkurin dawo da rangajin kasar Biyafara daga kungiyar IPOB, da kuma soma ragajin ballewar Yarabawa da yan Afenebire da su IGhaho ke jagoranta.
Duk da wannan barazanar dagewar yan kasar da ma shugabbani har yanzu Nijeriya tana nan a Nijeriya kasa daya mai bin tafarkin dimokaradiyya.
Nijeriya ta samu bunkasar tattalin arziki, musamman daga albarkacin kasa irin su Mayin-Fetru, wannan bunkasar tattalin arzikin ya sanya kasar na farko-farko a cigaban tattalin arziki a tsakanin kasashen Africa, dama sao’in ta masu tasowa a duniya.
Duk da Nijeriya ta samu sauye sauyen juyin mulki da kutseen sojojin wajen guda 7. A shekara 1999 Nijeriya ta dawo tafarkin dimokadiya, wanda yanzu za a iya cewa tafarkin dimokaradiya ya kafu a Nijeriya.
Amma ba a nan gizo ke sakar ba, hadin kan yan nijeriya a kan kasancewar ta kasa daya, ya zamanto babban kalubale a hannun jagorin dimokardiyayyar yau.
Bisa kasancewar Najeriya an hadata ne daga bangarori daban daban, kudu da arewa, wa yanda suke da kabilu daban-daban, addinai ma banbanta, kasar tafi kasancewa a dunkule a hannu shugabannin baya,musamma ma na soja a kan wannan lokacin da muke ciki.
Babban kalubalen da ke fuskantar Nijeriya shine dawo da karfin bangaranci da sanya addini wajen wa mulkar Nijeriya, wannan karon ya billo ta hannun gwamnionin jahohin nijeriya, wa yanda suka fi karfin fada aji a dimokaradiyyar Nijeriya.
Duka da kasan cewar wannan kalubalen yana da tarihi da kuma tunanin wasu shugabban nin na ganin cewa bawa kowa ne yanki dama wajen jagorancin Nijeriya zai kara dinke kasar wuri guda.
General Ibrahim Badamasi Babangida da ya mulki Nijeriya tsakanin 1984 – 1993, bayan yayi yunkurin maida kasar tafarkin dimokaradiyya wanda ya gagara a wancan lokacin bayan soke zaben June 12, ya maida mulkin kasar ga Mr. Ernest Shonikan a shekara 1993, wanda daga baya Ganeral Sani Abach ya kwace mulkin a hannun sa, Shonikan ya fito daga Kudu-Maso-Yamman Nijeriya, bisa la’akarin ‘yan arewa ne suka fi mulkar kasar a baya.
Shin za a iya cewa wannan ya kawo maslaha da hadin kan kasar? Ko kuma ya bude babin mulkin bangaranci ba la’akari da cancanta ba.
Duk da kasan cewar a wayanda suka mulki Nijeriya su 16 da 1960 zuwa yau, mutane 10 duk sun fito da ga Arewacin Nijeriya ne yayin da mutane 5 daga kudancin Nijeriya.
A yunku rin dawowa mulkin Dimokadiyya a shekarar 1999, ‘yan siyasar kasar sun karkata don maida mulkin kasar ga kudancin Nijeriya a yayin da a ka fitar da dukkanin yan takarar manyan jama’iyun kasar a wannan lokacin wato PDP da APP daga kudancin Nijeriya. A wannan lokacin an zabi Chief Olusegun Obasanjo 1999 a matsayin shugaban kasa.
Bayan yunkurin Obasanjo na zarcewa akan mulki ya gagagra a shekar 2007, jama’iyar PDP ta fiddo da tsarin karba-karba, yayin da mulki ya dawo arewa, amma fa duk wannan matsayin ya sabawa zahirin dimokadiyya, da kuma cusawa yan kasa tunanin kasa daya al’ummah daya.
A wani sabon salo a wannan lokacin, barazana da kasancewar zaman kasar nan dunkulalliyar kasa, bisa cusa ruhi tunani da duk yan kasa na sanya Nijeriya a gaba da komai yana neman chanja salo.
A wannan karon abin tashin hankali shine, yadda Gwamnonin wannan kasa suke kokarin raba kan yan kasa kan bukatar wanda zai mulki Nijeriya a zabe mai zuwa na 2023, bisa tsari na bangarancin kudu da arewa. Yayin da gwamnonin kudu suka ce dole sai shugabanci ya koma kudu. Su kuma gwamnonin arewa suka ce basu amince ba, tunda wannan ikirari ya sabawa kundin tsarin mulki da ma tsarin dimokaradiyya.
Kusan akasarin wannan gwamnoni suna jama’iyya daye ne walu PDP ko APC. Mun zaci za su sanya cancanta da matsalolin kasar a gaba wajen zakulo mata jagora, sai kawai suka bige da siyasar neman mulki ta hanyar bangaranci.
Yayin yin dogon nazari zamu ga wannan ikirari fa ya biyo bayan fadi tashin da akeyi na yunkurin raba Nijeriya da IPOB keyi bisa jagorancin Nmendi Kanu da yunkurin Afeneferi bisa jagorancin Mr. Igaho, wa yanda duk suke fuskantar shari’a a yanzu, shin kwa wadannan yunkurin ba kawai siyasa bace don neman mulki.
Abin da ke wajibi a wurin ‘yan Nijeriya a yau, shine kyakkyawan tunani da jagorancin bisa tafarkin cigaba na zamani da fidda kasar da kangin da take ciki na karayar tattalin arziki, kankin talauchi, uwa uba rashin tsaro, wanda wannan kadai ne zai dora kasar a kan tafarkin cigaba kamar sauran takwarorinta na duniya.
Wannan kawai zai faru ne in shugabann ni suka kau da san rai, kabilanci, babancin addini da samun tsannani kishin kasa, wajen zaben shugabnni bisa chanchanta ba wai kawai kallon bangaren da suka fito ba ko addinin su.
Irin wannan tunani na gwamnonin nan namu kan yi karfafa masu bore ko faan kabilanci da kullum yake addabar wannan kasar, wanda a zahirance yana nuna cewa koda su shugaban nin da suka fi kowa cin moriyar Nijeriya a wannan shekarun a kwai dattin kabilanci a zukatansu.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post