Sakamakon yawan sayen ‘data’ da matasa ke yi, kamfanin MTN ya bayyana samun cinikin da bai taɓa irin sa a Najeriya ba a cikin watanni 9.
Kamfanin MTN ya bayyana cewa ya samu cinikin naira tiriliyan 1.2 tsakanin Janairu zuwa Satumba a Najeriya. Haka dai wata sanarwa daga Hedikwatar MTN daga Afrika ta Kudu ta bayyana.
Ɗaya daga cikin babban jami’in MTN Mai suna Karl Toriola, ya bayyana cewa an samu cinikin na naira tiriliyan 1.2 cikin watanni 9 ne saboda yawan sayen data da ake yi.
Ya ce an samu riba ta naira biliyan 321.4 kenan a cikin watanni 9.
“Idan aka lissafa haraji kuwa aka cire kuɗin haraji, to ribar za ta koma naira biliyan 220.312 kenan.”
Cikin shekarar 2020 dai MTN ya yi cinikin naira tiriliyan 1.3 a Najeriya. Hakan na nufin cinikin zai haura wannan adadin sosai a cikin 2021, domin har an yi cinikin Naira Tiriliyan 1.2 a cikin watanni 9.
MTN ya sanar cewa masu sayen data sun ƙaru cikin watanni 9 da mutum miliyan 2.5.
“Masu sayen data ta MTN a yanzu sun kai mutum miliyan 33.2 tsakanin Janairu zuwa Satumba, 2021.”
Sai dai kuma sanarwar ta ce masu amfani da buga wayar layin MTN sun ragu da mutum miliyan 7.5. A yanzu mutum miliyan 67.5 ne ke amfani da layin MTN.
“Hakan kuwa na da nasaba da tsauraran matakan da aka ɗauka wajen kafin a yi wa layukan waya rajista a Najeriya.”
Discussion about this post