Tsohon ɗan jarida Dele Momudu ya yi sanarwar sake tsunduma cikin siyasa, bayan wani dogon hutu da ya yi na ƙaurace mata.
A cikin sanarwar, Mamudu ya bayyana cewa a yanzu ya yi rajista da jam’iyyar PDP.
Dele Momudu dai shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NCP a lokacin zaɓen 2011 na shugaban ƙasa.
Cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce ya shiga PDP domin ya taimaka a dawo da Najeriya bisa miƙaƙƙar hanya, tunda ya yanzu APC mai mulki ta ɗora ƙasar bisa karkatacciyar hanya.
“Na yanke shawarar daina yawan kuka da ƙorafin halin da ƙasar nan ke ciki. Na yi rajistar shiga a dama da ni da sauran ‘yan Najeriya masu kishi, domin a ceto ƙasar nan daga durƙushewa.” Haka Mamudu ya bayyana.
“Saboda haka dangane da abin da na ke yawan tsokaci a kai tsawon shekaru, ina da yaƙinin cewa sai na shiga cikin jam’iyyar adawa sannan zan iya taimakawa a samu canjin da na ke ta hanƙoron wasu su yi.
“Bayan na nemi shawarwari, ganin yadda ƙasar nan ke neman durƙushewa a ƙarƙashin wannan mulki, na yanke shawarar shiga jam’iyyar PDP.”
Dele Momudu ya ci gaba da kawo dalilai da su ka haɗa halin matsalar tsaro, matsalar tattalin arzikin ƙasa, tsadar rayuwa da mummunan kashe-kashen da ke faruwa a ƙarƙashin gwamnatin APC.
Mamudu ya nemi gafarar ‘yan Najeriya a kan muhimmiyar rawar da ya taka wajen ganin Buhari ya ci zaɓe a 2015.
Mamudu da mawallafin Sahara Reporters, Omoleye Sawore na daga cikin mashahuran ‘yan Najeriya da su ka mara wa Buhari baya, har ya samu nasara, a zaɓen 2015. Sun yi ƙaurin suna wajen ragargazar gwamnatin Jonathan a lokacin.
Discussion about this post