A zaman majalisar dokokin jihar Zamfara ranar Talata, majalisar ta dakatar da wasu mambobi biyu Ibrahim Tudu-Tukur (Bakura) da Yusuf Anka (Anka) saboda nuna murnar su kakara a lokacin da ‘yan bindiga suka sace mahaifin kakakin majalisar.
Kakakin majalisar Mustapha Jaafar, bayyana haka bayan kammala zama da majalisar ta yi a Gusau.
Jaafaru ya ce tuni an tunkuda su gaban Kwamitin tsawatarwa ta majalisar domin ta gudanar da bincike akai.
Dan majalisa Yusuf Kanoma wanda shine ya jagoranci mahawarar ranar Talata ya fadi a zauren majalisar cewa ‘yan majalisan su biyu wato Ibrahim da Yusuf Anka sun rika nuna murnan su da farinciki a lokacin da aka sace mahaifin Kakakin majalisar jihar.
” Sun yi ta nuna jin dadin su kakara a bainar jama’a suna farincikin sace mahaifin kakakin majalisar. Bayan haka akwai zaton da ake yi kila ma suna tare da ‘yan bindigan da suka sace shi ne.
Wannan shine dalilin da ya sa majalisar ta dakatar da su ‘yan majalisar domin a yi bincike akan su.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka sace mahaifin kakakin majalisar jihar Zamfara a kauyen Magarya.