Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi ƙara yawan kasafin 2022 daga naira tiriliyan 13.98 zuwa naira tiriliyan 16.45
Wannan ƙoƙon bara ya na kunshe cikin wata wasiƙar da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan a ranar Talata.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ovie Omo-Agege ne ya karanta wasiƙa a Zauren Majalisa.
A ranar Alhamis ne Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da kuma karanta kasafin 2022 a gaban haɗakar dukkan Mambobin Majalisar Dattawa da na Majalisar Tarayya.
A cikin wasiƙar dai Buhari ya nemi amincewar Majalisa domin ya yi wasu ƙare-ƙare a wasu ɓangarorin ayyuka na kurkusa.
Buhari ya ce sabuwar Dokar Fetur (PIA), wacce aka sa wa hannu wata biyu da su ka wuce, ita ce ta haddasa yin ƙarin kasafin.
Daga cikin ƙarin da Buhari ya nemi a yi, akwai yi wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ƙarin Naira biliyan 100 domin ƙara kimtsi da shirin gudanar da zaɓen 2023.
Sannan kuma akwai ƙarin naira biliyan 510 ga Shirin Rage Raɗadin Fatara a cikin ƙasa.
Discussion about this post