Wani likitan mata da ya kware a wajen kula da mata masu ciki, haihuwa da jego, Akinsola Akinde ya gargaɗi mata da su daina cin mahaifa ko mabiyiya kamar yadda wasu ke kiran sa bayan sun haihu wai don kara lafiya da ruwan nono.
Akinde ya yi wannan gargadi ne da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Litini a jihar Legas.
Ya ce mahaifa ko mabiyiya na manne ne a jikin rumbun mahaifa wanda ke hada cibiyar jariri. Shine yake kai masa abinci da iskar da yake shaka da dai sauransu.
Akinde ya ce a dalilin haka wannan nama ke zama dafi domin yana dauke da kwayoyin cutar bacteria wanda idan ya fito bayan an haihu yqnke shi ya kamata a yi a jefar da shi ba kuma aci ba.
Likitan ya ce ya yi wannan kira ne ganin yadda wasu fitattun mata a kasashen Turai ke nunawa a yanar gizo cewa cin mahaifa ko mabiyiya wajen mai jego na inganta lafiyar ta da na jaririn da aka haifa.
“A cewar masu ci wai mahaifa na da sinadarin Protein da fats wanda ke taimakawa wajen kara ruwan nono tare da inganta lafiyar Uwa da jariri.
“Sun ce mai jego za ta iya cin wannan mahaifa ko mabiyiya danye, dafaffe, gasasshhe ko kuma a busar da shi a daka shi lukui mai jego na cin shi.
Akinde ya ce wannan magana ba gaskiya ba ce domin babu wani bincike da aka taba yi daga wasu kwararru da ya nuna wai cin mahaifa na da amfani ga maijego.
Ya yi kira ga matan Afrika da su daina ci su yi hakuri har sai an yi bincike an kuma tabbatar da amfanin cin sa da rashin cin sa ka fin nan su sami madafa.
Discussion about this post