Hukumar Rarraba Kuɗaɗe ta Ƙasa, wato ‘Revenue Mobilisation and Fiscal Commission’ (RMFAC), ta fara aikin shirin sake fasalin rabon kuɗaɗen gwamnati ga tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi, a yau Litinin.
Za a fara shirin da gabatar da taron jin ra’ayoyin jama’a kai-tsaye a Legas.
Cikin wata sanarwa da hukumar RMFAC ta fitar ta ce taron jin ra’ayoyin jama’a da za a fara na yankin Kudu maso Gabas a Legas, kai kasance wanda zai buɗe ƙofar fito da sabon tsarin raba kuɗaɗe a ƙasar nan.
Jihohin da za su yi jawabai a taron Legas sun haɗa da Legas, Ekiti, Oyo, Ogun, Osun da Ondo.
A ƙarƙashin tsarin raba kuɗaɗen da ake a kai, gwamnatin tarayya ce ke kwasar kashi 52.68 na kuɗaɗen shigar da ake tarawa duk wata.
Yayin da ake bai wa jihohi kashi 26.72, su kuma ƙananan hukumomi ana lasa masu kashi 20.60 na kuɗaɗen.
Hukumar ta ce dama dokar ƙasa ce ta ba ta ikon sake nazari tare da tsarin rabon kuɗaɗen a kai a kai, domin a riƙa tabbatar da ana samun daidaito, a yanayin da aka tsinci kai a ciki.
Taron yankin Kudu maso Kudu zai gudana ne a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas a ranar Alhamis, 7 Ga Oktoba da washegari 8 Ga wata.
Zai fitar da masu bayar da ra’ayoyin su daga jihohin Ribas, Akwa Igbom, Bayelsa, Delta da Edo da Cross Rivers.
A yankin Kudu maso Gabas kuwa zai gudana ne a Jihar Imo a ranakun 11 da 12 Ga Okotoba. Akwai Anambra, Ebonyi, Enugu, da Imo.
A Kaduna za a yi taron ɓangaren Arewa ta Yamma, wato jihohin Kaduna, Kano, Jigawa, Katsina, Sokoto da Zamfara.
A jihar Kogi za a yi taron shiyyar Arewa ta Tsakiya a ranakun 19 zuwa 20 Ga Oktoba, wanda zai samu halartar jihohin da su ka haɗa da Benuwai, Kwara, Nasarawa, Neja da Filato.
Sai kuma taron Arewa maso Gabas da za a yi ranakun 21 da 22 Ga Oktoba. Wato na wakilan jihohin Adamawa, Bauchi, Barno, Taraba, da Yobe.
A babban Birnin Tarayya kuwa, za a saurari ra’ayoyin jama’a a ranakun 25 zuwa 26 Ga Oktoba.
Waɗanda za su halarci tarukan za su fito daga ɓangarorin gwamnatin jihohi, majalisu, ƙananan hukumomi, ƙungiyoyin jama’a, ƙungiyoyin ma’aikata, dattawa, manyan ƙasa, sarakunan gargajiya da sauran jama’ar gari.
Ana buƙatar duk wanda ke buƙatar gabatar da na sa ra’ayi ya aika da kwafe biyar na bugaggen rubutun sa a takarda da kuma ta saƙon e-mel.