A ranar Juma’a babban kotu a Ibadan ta yanke wa wani dan fara dake wafce wa mutane kudade ta hanyar gizo hukuncin share harabar kotu na tsawon watanni shida.
Kotun ta kama Tosin da laifin damfarar wani dar kasan Amurka mai suna Lylian Zamarippa dala 2,400.
Bisa ga hukuncin da alkali Bayo Taiwo ya yanke Tosin zai rika sharar harabar kotun daga karfe 8 na safe zuwa 12 rana sau biyar a mako.
Alkali Taiwo ya ce Tosin zai yi zaman kurkuku na tsawon shekara biyu idan har bai zo ya yi sharar ba ko kuma idan ya yi lati koda na ranar karshe ne.
Ya kuma ce Tosin zai mayar wa dan kasar Amurka da ya damfara dala 2,400 kudin sa sannan gwamnati za ta kwace motarsa kiran SUV, komfutar sa da wayar salulansa.
Lauyan da ya shigar da karan Festus Ojo, ya bayyana cewa Tosin ya aikata wannan laifi ne takanin watan Faburairu 2020 da Janairu 2021.
Ya ce Tosin ya yi wa dan kasar Amurka karyar cewa shi mace ce, sunan sa Zielone Nyson Kuma yana bukatar ya taimaka masa da kudi.
Daga nan lauyan dake kare Tosin M.A. Rufai ya roki sassauci daga wajen kotun tare da bai wa Tosin beli amma alkalin ya yi watsi da haka.
A wannan rana kuma alkalin kotun ya yanke wa wani mai sana’a irin na Tosin, Tunde Adejuwon shima hukuncin sharar kotu na tsawon watanni biyar.
Alkalin ya ce gwamnatin tarayya za ta kwace motar sa kira Lexus da wayar salulansa shima.
Discussion about this post