Tsohon shugaban majalisar dattawa Anyim Pius Anyim ya bayyana cewa ko da tsarin karba-karba ko babu zai yi takarar shugaban kasa a 2023.
Anyim ya kara da cewa jam’iyyar bata ce ga bangaren da dole sune za su yi takarar shugaban kasa ba. ” Abinda na sani shine kujerun mukamai na jam’iyyar ne aka karkasu su zuwa shiyyoyin kasar nan amma ga dukkan alamu takarar shugaban kasa kowa zai iya nema daga kowacce yankin kasar nan.
” A baya an rika buga fastocina na takarar shugaban kasa, amma kuma na yi hannun riga da hakan saboda ni a gani na lokacin bayyana ra’ayin takara bai yi ba.
” Yanzu ya rage wata 18 ne kacal wadanda suke kan mulki su tattara su kara gaba. Lokaci yayi in bayyana matsayina da burina ga ‘yan Najeriya. Saboda haka kowa ya sani zan fito takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.
Bayan ya yi shugaban majalisa a tsakanin 2000 zuwa 2003, anyim ya zama sakataren gwamnatin tarayya a lokacin mulkin Jonathan.
A cikin makon jiya, hukumar EFCC ta gayyaci Anyim inda ya bayyana a gabanta domin amsa wasu tambayoyi game da wasu harkalla da ake zargin ya aikata a lokacin da yake sakataren gwamnatin tarayya.
Anyim na daga cikin dakarun yan siyasan da ake ganin za su yi tasiri a yankin kudu maso Gasas a zaben 2023.