Karamin ministan lafiya Olorunnimbe Mamora ya yi kira ga manyan asibitocin gwamnati da ake da su su rika kula da cibiyoyin kiwon lafiya akalla biyu dake kusa da su a faɗin kasar nan.
Mamora ya fadi haka ne bisa ga tanadin da dokar kasar nan ta yi cewa manyan asibitoci su rika daukan nauyin kananan asibitoci.
Ya fadi haka ne a taron tattauna gina asibitin gwamnatin tarayya FMC a Deba jihar Gombe da kwamitin kiwon lafiya na majalisar dattawa ta shirya.
Gwamnati za ta kashe akalla Naira biliyan daya wajen gina wannan asibiti a jihar.
Bisa ga jawabin da Sanata Danjuma Goje yayi ya ce gina asibitin zai taimaka wajen inganta kiwon lafiyar mutane tare da horas da jami’an lafiya a jihar da kasa baki daya.
Goje ya ce majalisar dattawa na da cikakken sani kan yadda mutane ke fama da matsalar rashin samun kiwon lafiya duk da manyan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko da ake da su a kasar nan.
Mamora ya ce gina asibitin FMC domin inganta lafiyar da mutane ke samu na da mahimmancin sai dai babu dokar da aka kafa da ya bada izinin gina asibitoci irin haka sannan da dokar da zai rika kula da aiyukkanta aibitin a yanzu haka.
“A kasar nan akwai dokar da ta bada damar gina asibitin koyarwa amma kuma kada a manta a jihar Gombe akwai asibiti mallakin gwamnatin tarayya dake aiki a jihar.
Maimakon a rika gina wasu,a rika amfani da kudaden ne wajen inganta wadanda ake da su da fadada su. Sannan da bunƙasa cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko dake fadin kasar nan.