‘Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kutsa ƙauyen Unguwar Samanja a daidai lokacin da ake shirin Sallar Asubahi, a ranar Litinin.
An tabbatar da cewa sun riƙa buɗe wa mutane wuta, har su ka kashe mutum shida nan take, kuma su ka arce da wasu a matsayin sun yi garkuwa da su.
Unguwar Samanja ta na kusa da garin Daudawa a Ƙaramar Hukumar Faskari.
Daudawa can ne aka haifi marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Umaru ‘Yar’Adua, lokacin da mahaifin sa ya je aiki can daga Katsina.
Jihar Katsina can kuma ne mahaifar Shugaba Muhammadu Buhari. Amma matsalar tsaro ta yi wa jihar ɗaurin-gwarmai, ta gagari waɗanda haƙƙin shawo kan lamarin ya rataya a wuyan su.
Wasu mazauna garin Daudawa da ke kusa da Unguwar Samanja inda aka kai farmakin, sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun isa Unguwar Samanja wajen ƙarfe 5.49, kuma a kan babura su ka je, kowane ɗauke da muggan makamai.
Sun isa a lokacin da ake ta shirye-shiryen alwalar Sallar Asubahi.
Ita ma ƙaramar hukumar Faskari ta sha fama da ‘yan bindiga tsawon shekaru.
Kuma ta na cikin Ƙananan Hukumomi 13 da aka yanke wa hanyoyin sadarwar waya a jihar Katsina.
Wata ƙungiya a cikin garin Daudawa ta yi kukan cewa duk da matakan tsaron da ake cewa ana ɗauka, har yau ba a daina kai hare-hare a yankunan Ƙaramar Hukumar Faskari ba.
Wani mazaunin Daudawa mai suna Nasir Hassan, ya ce ‘yan bindigar sun dira ƙauyen a kan jerin-gwanon babura, inda su na shiga garin su ka riƙa darzaza harbin bindigogi, duk aka ruɗe.
“Daga sahihin labarin da na ji, sun kashe mutum biyar, waɗanda aka rufe yau Litinin.”
Hassan wanda ɗalibin gaba da sakandare ne a wata makaranta a jihar Zamfara, ya ce “maharan sun kuma ƙone gidaje, sun ƙone shagunan sayar da kayan abinci da kayan masarufi.
“An shaida min cewa ba su kwashi kayan kowa ba, sun dai kona shagunan sayar da kayan abinci da masarufi.”
Amma wani mai suna Auwal Liman, wanda shi ma mutumin Daudawa ɗin ne, ya shaida wa wakilin mu cewa waɗanda aka kashe sun fi mutum shida, domin a daidai shiga garin Unguwar Samanja ma maharan sun harbe wani mutumin Unguwar Labbo.
Bahisulhaq Alhassan wanda ɗalibi ne a Faskari, ya shaida wa wakilin mu cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe ɗin ma abokin sa ne mai suna Ja’afar Kabir can a Unguwar Samanja ɗin.
Wakilin PREMIUM TIMES ya kira lambar Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Gambo Isa, amma bai ɗauki waya ba. Kuma ya tura masa saƙon tes, shi ma bai maida masa amsa ba.