A ranar Juma’a ne Najeriya ta karbi gudunmawar kwalaben ruwan maganin rigakafin cutar korona na AstraZeneca 501,600 daga kasar Faransa.
Asusun COVAX ne ta yi jigilar magungunan zuwa Najeriya daga kasar Faransa sannan tuni har an adana su a wurin ajiyar maganin rigakafin da gwamnati tarayya ta samar a tashar jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya ce wannan gudunmawar ya nuna goyan baya da kasar Faransa ke yi kan yaki da cutar da Najeriya ke yi.
Shu’aib ya tabbatar cewa gwamnati ta samar da ingantattun wuraren ajiyar maganin rigakafin cutar.
Shu’aib ya kara da cewa gwamnati ta tsara hanyoyi da za su taimaka wajen tabbatar da an yi wa mutane allurar rigakafin da magungunan a duk jihohin dake kasar nan.
Bayan haka jakadan kasar Faransa a NAjeriya Jerome Pasquier ya jinjina kokarin da kwamitin PSC ta yi na yaki da cutar a kasar.
Pasquier ya yi kira ga wadanda ba su yi allurar rigakafin ba su hanzarta zuwa wuraren da ake yin rigakafin su yi suma.
Ya ce Kasar Faransa Bata bukata mutum ya yi gwajin korona bayan ya yi allurar rigakafin cutar domin katin shaidar yin allurar rigakafin ne kadai mutum zai bukata a lokacin da zai shiga kasar.
Discussion about this post