Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da ciwo bashi da ga waje domin kammala wasu ayyuka da gwamnati ke yi a kasar nan.
Buhari ya ce za a ciyo bashi domin cike gibin kasafin kudin 2022.
A jawabin sa a lokacin da yake bayyana kasafin ga ‘yan majalisan dalla-dalla ya ce kasafin 2022 zai mayar da hankali ne wajen kammala ayyukan da aka soma.
Sannan kuma fannin tsaro da ilimi sun samu kaso masu tsoka a cikin wannan kasafi.
Gwamnatin Najeriya za ta ciwo bashin Naira tiriliyan 5.012 domin cike giɓin kasafin ƙuɗi na 2022.
Hakan na nufin ana tafiyar ci gaban mai ginin rijiya, ya na dannawa ƙasa, shi kuma ya na cewa gaba ya ke yi.
Yayin da gwamnatin tarayya ke cewa har yanzu bashin da ta ke ciwowa ba mai kumbura ciki ba ne, a gefe ɗaya kuma kuɗaɗen shiga da suka haɗa da ribar mai da haraji mafi yawa su na tafiya ne wajen bashin da ake riƙa biya a hankali duk ƙarshen wata.
Discussion about this post