Shugaban ofishin Jakadancin kasar Amurka CDA Kathleen FitzGibbon ta bayyana cewa jihar Abia ce jiha ta shida da ta fi yawan mutanen dake dauke da cutar kanjamau a Najeriya.
Kathleen ta fadi haka ranar Talata a taron dakile yaduwar cutar da CDA ta yi da gidauniyar ‘Catholic Caritas’ da gwamnatin jihar Abia a garin Ummahia.
A lissafe dai mutum 58,341 ne ke dauke da cutar a jihar.
Ta ce kasar Amurka a shirye take ta ci gaba da tallafa wa gwamnati wajen yaki da cutar a jihar.
“CDA ta shirya don daukar nauyin mutum 37,000 dake dauke da cutar daga nan zuwa shekaru biyu masu zuwa.
“Kanjamau ba mutuwa bane kamar yadda ake ta fadi tun shekaru 20 da suka wuce.
“Zuwa yanzu mutum miliyan 1.6 dake dauke da cutar na karbar magani sannan suna rayuwar su cikin koshin lafiya a Najeriya.
Bayan haka gwamnan jihar Okezie Ikpeazu ya ce jihar Abia na da iyakan ƙasa da jihohi bakwai da suma suke fama da yawan mutanen dake fama da cutar.
Ikpeazu ya ce gwamnati ta dauki matakan da za su taimaka wajen hana mutane shiga jihar da cutar.
Babban limamin cocin darikan katolika Lucius Ugorji ya ce cocin su za ta mai da hankali wajen wayar da kan mutane illar dake tattare da nuna wa masu fama da cutar wariya.
Discussion about this post