Jami’ar Kaduna ta dakatar da wasu daliban makarantar da suka yi wa daliban makarantar sojoji ribiti a taron marabtan sabin dalibai Jami’ar da aka yi ranar 12 ga Oktoba.
Kakakin Jami’ar Adamu Bargo da ya sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba a garin Kaduna ya ce daliban sun yi wa sojojin taron dangi suka rika sirfarsu har suka farfasa musu motar da suka zo da shi.
Bargo ya ce wannan rikici ya auku ne a lokacin da ake taron marabtan sabin dalibai da Jami’ar ta dauka inda wani daga cikin daliban sojoji ya ga wata budurwa ya nemi ta bashi lambarta shikenan fa sai yamutsi ya barke.
“Ashe wannan budurwa na tare da saurayinta ne dalilin da ya sa bata kula sojan ba.
“Da dalibin sojan ya ga burwar ta ki kula shi sai ya nemi ya karbi lambar ta karfi da tsiya. Da saurayin da ke tsaye da ita ya nemi yi wa sojan magana sai ya sharara masa mari.
“Bayan sojan ya dalla wa saurayin budurwar mari sai shi kuma ya kira abokansa dalibai suka rika jibgar sojan sannan suka kuma lalata masa mota kirar Toyota Matrix.
Bargo ya ce Jami’ar ta fara gudanar da bincike kan abin da ya faru kuma ta dakatar da daliban da suka yi wa sojan taron dangi a makarantar.
Ya kuma ce Jami’ar ta saka wasu matakai da za su taimaka wajen hana aukuwar abinda ya faru.