Karin maganar da ake cewa fatara da talauci da yunwa sun fi raina na kwance, domin shi ya fi saurin dannewa, to karin maganar ba za ta yi tasiri ba a wurin Theresa Paul, matar da rashin galihu bai kore ta daga harkokin noma ba, sai ma ƙara mata ƙaimin juriya ya yi.
Theresa wadda ke noma a yankin karkarar Abuja, ya zabura domin rufa wa kan ta asiri, inda ta rungumi harkar noma ka’in-da-na’in.
“Shekara takwas kenan ina noma, ina kiwo. Ina noman masara, wake da rogo. Sannan kuma ina kiwon kaji.
“Na shiga harkar noma don na tallafi iyalin na kuma na ga na riƙa samun ‘yan kuɗin ɓatarwa da biyan sauran buƙatu na dole. Idan kaka ta yi, na kan girbe amfanin gonar da na samu, a gyara sannan na kai kasuwar Kuje na sayar. Kuma ina sayar da ƙwayayen kaji, tunda ina kiwon kajin.”
Ta ci gaba da shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba gona gare ta ba, tunda ita ma zama ya kai ta zama cikin ƙabilar Gwarawa a Abuja.
Ta ce a hannun Gwarawa ta ke karɓar aron gona ta biya da kuɗin ta. “Akwai wadda zan karɓi aro Naira 10,000. Ya danganta, wata ma har Naira 2,000 kacal a duk fuloti ɗaya.
Ta bada labarin yadda makiyaya su ka hana ta sakat a gonar ta. Ta ce akwai ma wani lokaci a cikin 2019 makiyayan da ke mata ɓarna su ka cinna mata shanu su ka bi ta a guje, har ta faɗi ta goce hannu ɗaya.
Ta ce a yanzu haka hannun wanda ta ji ciwo da shi, ba ta iya aiki sosai da shi.
Tsananin rashin kuɗi bai sa Theresa ta yi watsi da noma ba. Domin ta ce ko takin zamani ba ta da ƙarfin saye, sai dai ta yi amfani da takin kashin kajin da ta ke kiwo.
Theresa ta ce ta shiga cikin ƙungiyoyin mata manoma, amma har yau ba ta taɓa cin moriyar ko sisi dalilin ƙungiya ba.
Ta ce ‘yan ga-noma ta ke kira su yi mata noma a gona, tunda ba ta da halin biyan kuɗin noman zamani. Ta kan kashe har naira 20,000 wajen noman.
“Ina fuskantar matsaloli da dama a harkar noman nan. Ka ga dai ga matsalar ƙwarin wake da ƙwarin da ke cinye masara. Wato abin ni dai ya zame min wahala daga wannan sai wannan. Idan wannan shekara na fuskanci ƙwarin wake, wata shekara kuma matsalar makiyaya. Sannan a duk shekara ina fama da ƙarancin kudin aikin noma.”
Ta ce ba ta taɓa sanin akwai FADAMA ba, sai kwanan nan, lokacin da wasu mata su ka ja ni mu ka je wani taron manoma a Gwagwalada, inda aka raba mana maganin ƙwari da kuma famfon feshin maganin ƙwarin.” Inji Theresa.
Discussion about this post