Najeriya ta amince a fara gwaji tare da noman sabon nau’in irin nasarar da Cibiyar Binciken Dabarun Noma ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta ƙirƙiro.
Wannan nau’in iri masara dai tsutsotsi da ƙwari ba su iya yi masa lahani, kuma shukar sa na jimirin ƙarancin ruwa sosai.
Wannan umarnin amincewa na ƙunshe ne cikin katin shaidar da Hukumar Binciken Ingancin Kayan Gona ta Ƙasa (NBMA) ta bai wa Cibiyar Binciken Kayan Gona (IAR) ta ABU.
NBMA ce ke da alhakin bincike da tantance lafiya da ingancin irin shukar da aka ƙirƙiro ta hanyar dabarun zamani.
An bai wa IAR wannan katin shaida tun a ranar 8 Ga Oktoba, 2021, mai lamba NBMA/CM/003.
Irin Masarar TELA Mai Jure Fari: Wannan irin masara da aka ƙirƙiro a Cibiyar IAR da ke Jami’ar Ahmadu Bello ta Zari’a, an ƙirƙiro shi ne yadda zai iya jure ƙarancin ruwa, ba tare da ya bushe ba. Kuma tsutsotsi ba su iya lahanta shi. Za a yi shekara huɗu ana jaraba shi, daga 8 Ga Oktoba 2021 zuwa 5 Ga Oktoba, 2024.
Yayin bayar da shaidar amincewar, an yi amfani da shawarwarin da kwamitin NBT ya bayar da kuma yin la’akari da ko akwai wata illa ko babu idan aka yi kasadar bayar da izinin.
“Wannan hukuma ta gamsu cewa jaraba wanann irin masara na TELA ba zai yi wa gonaki ko yanayi wata illa ba.”
Da ya ke bayani bayan an bayar da umarnin, Shugaban Cibiyar Binciken Dabarun Noma (IAR), Farfesa Ishiyaku Mohammed, ya bayyana cewa abin ci gaba ne matuƙa da samun ƙwarin guiwa, ganin yadda IAR ta samu amincewar shuka wannan irin masara daga hukumar NBMA.
Ishiyaku ya ce Cibiyar Binciken Dabarun Noma za ta ci gaba da bayar da gagarimar gudummawa domin magance matsalolin da manoma ke fuskanta a faɗin ƙasar nan.
Ya ce daga nan kuma mataki na gaba shi ne za a nemi amincewar kwamiti kafin a fara sayar wa manoma irin nasarar, domin domin su shuka a daminar shekarar 2023.
Babban Daraktan AATF, Canisius Kanangire, ya ce “Irin Masarar TELA ya zo daidai lokacin da manoma ke ta faman fafutikar kashe kuɗaɗe masu yawa wajen fatattakar ƙwari da tsutsotsi.
Kuma zai magance matsalar ƙarancin ruwan sama a lokacin fari. Sannan kuma za su rage yawan amfani da maganin feshin ƙwari, wanda barazana ne ga lafiyar jama’a.” Inji Kanangire.