Kamfanin motoci na Tesla ya shiga sahun kamfanoni biyar na duniya, waɗanda jarin su ya kai dala tiriliyan 1 kowanen su.
Jarin Tesla ya kai dala tiriliyan 1 a cikin wannan makon bayan ya ƙaru da kashi 12.6 bisa 100, sakamakon yarjejeniyar da kamfanin ya ƙulla da kamfanin bada hayar motoci na Hertz, wanda zai sayi motoci 100,000 masu aiki da wutar lantarki daga Tesla.
Tuni dai har Hertz ya biya dala biliyan 4 daga cikin kuɗaɗen.
Sanadiyar wannan ciniki, Shugaban Kamfanin Tesla Elon Musk, ya samu ƙarin jarin dala biliyan 36 a rana ɗaya kenan.
Wannan ƙarin dala biliyan 36 da ya samu a rana ɗaya, ta fi kuɗin da Aliko Ɗangote ya ke da shi, wanda a lissafin cikin watan Satumba, shi ne na 117 a jerin attajiran duniya, kuma ya mallaki dala biliyan 17.
Kowace dala biliyan 1 daidai ta ke da Naira biliyan 500 da ɗoriya.
Yayin da Elon Musk ya samu dala biliyan 36 a rana ɗaya, kasafin kuɗin Najeriya na 2021 kuma dala biliyan 37, daidai da naira tiriliyan 16.39 kenan.
Kafin Musk ya samu ƙarin jarin dala biliyan 36 a rana ɗaya, shi ne na 1 a jerin attajiran duniya da dala biliyan 194. Yanzu kuwa ya zama ya na da dala biliyan 230 kenan.
2. Na biyu a jerin attajiran duniya dai shi ne Jeff Bezos mai amfanin Amazon, wanda ya mallaki jarin dala biliyan 194.
3. Na uku mutumin ƙasar Faransa ne mai suna Bernard Anold, wanda ya mallaki dala biliyan 174.
4. Bill Gates wanda a baya ya daɗe a matsayin babban ƙasaitaccen attajiri na farko a duniya, yanzu ya koma na huɗu, inda ya ke da dala biliyan 149, bayan an kamfaci kuɗin sa an ba tsohuwar matar sa Melinda matsayin kuɗin kishin-laifin tsinka igiyar auren su.
5. Na biyar kuma shi ne mai kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg, wanda ya mallaki jarin dala biliyan 132.
6. Na shida Larry Page, ɗaya daga cikin waɗanda su ka ƙirƙiro Google, wanda ke da dala biliyan 124.
7. Na bakwai Sergie Brin, abokin Larry Page, wanda su ka ƙirƙiro Google tare, mai jarin dala biliyan 119.
10. Shi ne Warren Buffet, mai jarin dala biliyan 100.
117. Na 117 kuma Aliko Ɗangote, mai jarin dala biliyan 17.
Sauran kamfanonin da jarin kowanen su ya kai dala tiriliyan 1 kuwa banda Tesla, su ne Apple, Microsoft, Amazon, Alphabet da kuma Aramco.