Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi ƙarin haske game da matsayar gwamnonin Arewa akan takarar shugabancin Najeriya bayan Buhari ya kammala wa’adin sa a 2023.
A wasu tambayoyi da ya amsa kan haka da wasu al’amuran da suka shafi jihar Kaduna ya ce gwamnonin ba su ki mulki ya koma kudu ba.
El-Rufai ya ce kawai sai gwamnonin kudu su rika cewa dole sai an mika musu mulki, haka kawai ba tare da sun yi abin da ya dace ba don samun goyon bayanmu da na mutanen mu.
” Ina daga cikin waɗanda suka fito tun a 2019 suka bayyana ra’ayin su game da tsarin karɓa-karɓa da kuma mara wa hakan baya. Ni a ganina yin haka zai kara kawo haɗin kai ne a ƙasar nan. Abinda naga bai dace ba kuma ba zamu yarda da shi ba shine kalmar ‘dole’ da gwamnonin kudu ke amfani da shi a kullum aka zo maganar takarar shugabancin Najeriya.
” Wannan abu ne da babu tilas a cikin sa, zama ake yi a tattauna, a nemi yin sulhu da kuma hadin kai da goyon baya.
” Abinda gwamnonin Arewa suka yi shine ja musu kunne da nuna rashin jin daɗin mu kan yadda suke amfani da kalmar ‘dole’ idan suka zo faɗin matsayin su game da takarar shugabancin Najeriya. Ba karɓa-karɓar ba ce ba mu so, yadda suke murza gashin baki ne, su zazzaro idanu suna ciccin magani suna bubbuɗawa, ‘dole’ su za a baiwa takara ne ba mu amince da ba, haka kawai!
” Abubuwan da gidajen ƴaɗa labarai suka buga ya saɓa wa abubuwan da muka tattauna. Sannan kuma ma zamar ba wannan batu bane ke kan gaba da muke tattaunawa a wurin wannan taro.
” Tabbas mun tattauna akan irin kalaman da gwamnonin yankin kudu suke amfani da su wajen nuna maitansu game da kujerar shugaban kasa. Sai su rika bugun ƙirji suna cewa dole a basu takarar shugaban kasa a zaɓe mai zuwa. Haka ne bai yi mana daɗi ba muka ga ya dace mu fito mu faɗi musu abinda ya dace.
” Ko Arewa na so ko ba su so, dole kawai a basu takarar shugaban kasa. Menene ya kawo maganar dole a siyasa. A siyasa zama ake yi a tattauna a samu daidaituwa a tsakani. Arewa ta mara wa Olusegun Obasanjo baya, Arewa ta mara wa Jonathan baya kuma dukkan su ƴan kudu ne suka shugabanci Najeriya.
“Babu inda aka ce dole sai an yi karɓa-ƙarba a kundin tsarin mulkin Najeriya. Wasu ne suka ga ya dace ayi haka kuma aka yi don a samu haɗin kai.
“Kowacce jam’iyya ta na da nata salon mulkin da dokokin da ta tsara wa jam’iyyar ta. Mu a APC babu tsarin ƙarba-ƙarba. Ko su PDP din da suka ce sai dai ayi karɓar-Karɓar ba su yi amfani da ita ba lokacin Jonathan.
” Babu inda dokar Najeriya ta amince a yi tsarin karɓa-karɓa a kasar nan. Kowa yana da ikon ya nemi shugabancin Najeriya daga kowani yankin ƙasar nan. Saboda haka me ya kawo a rika amfani da ‘kalmar dole’. Kuma ku da kanku kun sani ba ku da madogara.
” Gwamnonin Arewa da dama sun fito sun kuma ce suna goyon bayan idan Buhari ya kammala wa’adin mulkin sa, mulki ya koma kudu. Mun faɗi haka ba wai don babu wanda ya cancanta bane daga Arewa. Kuma ko da na fada a lokacin wasu da yawa ba su ji daɗi ba. Wasu gwamnonin yankin duk sun faɗi irin haka
” Abinda muke so su sani shine ba ma musu bakin cikin mulki ya koma kudu bayan Buhari, amma kuma fa ba su rika cewa, dole, akan me za su riƙa cewa dole?