Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas na Najeriya sun bayar da gudunmawar kuɗi Naira miliyan 20, ga iyalan waɗanda ‘yan bindiga su ka kashe a kasuwar Goronyo ta Jihar Sokoto.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga yadda masu garkuwa da mutane su ka kai hari a kasuwar Goronyo, su ka buɗe wuta a ranar 17 Ga Oktoba, su ka kashe mutum 49. Tare kuma da jikkata da dama daga masu cin kasuwar.
Sai dai kuma wani rahoto da jaridar Daily Trust ta buga, bayan kwana biyu da kashe mutanen, ta ruwaito gogarman mai safarar manyan bindigogi Shehu Rakeb ya ce sun kai harin ne a matsayin ramuwar-gayyar kisan Fulani su 22 da aka yi a Unguwar Lalle, a lokacin da su ke Sallah.
Shehu Rakeb ya ce waɗanda ‘yan banga su ka kashe Fulani ne, amma ba ‘yan bindiga ba ne.
Ya kuma yi tir da yadda ake kiran su ‘yan ta’adda, amma kuma ba a kiran masu kashe Fulanin da ba su ji ba, ba su gani ba ‘yan ta’adda.
Yayin bayar da tallafin kuɗin, Gwamna Babagana Zulum, wanda ya yi sanarwar bayar da kuɗaɗen a madadin sauran gwamnonin yankin Arewa maso Gabas, ya isa Sokoto domin yin ta’aziyya ce tare da takwaran sa Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.
Sun yi ta’aziyya tare da jajantawa da kuma bayar da shawarwari.
Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ya nuna godiyar sa matuƙa. Inda ya ce ‘yan bindigar sun yi kaka-gida a Jihar Sokoto bayan sun tsere daga ɓarin wutar da Sojoji ke ki masu a Jihar Zamfara.
A kan haka, sai Tambuwal ya roƙi gwamnatin tarayya ta turo dakarun sojojin sama a Sokoto, domin su kakkaɓe ‘yan bindigar da su ka yi hijira daga Zamfara zuwa Sokoto.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga yadda rundunonin gogarma Bello Turji, Halilu ‘Roket’ da Shehu Rakeb su ka fice daga dajin Zamfara su ka koma dajin Sububu cikin jihar Sokoto.
Tambuwal ya kuma roƙi gwamnatin tarayya a buɗe layukan wayoyin da aka kulle a ƙananan hukumomi 14 na jihar Sokoto.