Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) ta fito da daftarin da zai hana duk wani yaro ko yarinya da ba su kai shekaru 18 ba mallakar layin waya a Najeriya.
Sabuwar ƙa’idar wadda aka fito da ita an bijiro da ita ne kwanan nan a hukumar a Abuja.
Dokar na cikin ƙudirorin doka uku da su ka haɗa har da ƙa’idar masu mallakar waya, dokar ƙa’idojin mallakar layin waya da kuma dokar ƙa’idar tsarin hada-hadar ‘spectrum’.
Dokar ta ce, “Sai Wanda Ya Kai Shekaru 18 Ke Da Iznin Yi Wa Rajistar Mallakar Layin Waya a Najeriya.”
A Najeriya dai babu wata dokar da ake bi ta ƙayyade yawan shekarun masu layin waya. Wannan ne ya sa ɗimbin ƙananan yara, musamman ƙananan ‘yan mata su ka mallaki wayoyi birjik.
A soshiyal midiya, musamman a Instagram da tik tok, ƙananan ‘yan mata sun yi kaka-gida su na sharholiya da taɓara, su na watsawa a duniya.
An dai bijiro da wannan doka a bisa yadda Sashe na 70 na Dokar Sadarwa ta Najeriya, ta 2003 ta gindaya sharaɗi.
Sannan kuma a ƙarƙashin wannan sabon tsarin, za a toshe hanyar da dillalan rajistar layuka ke sani ko mallakar bayanan masu layukan wayoyin hannu.
Dokar ta shimfiɗa ƙa’idojin da za su dora tsarin kiran wayoyin Najeriya daga nan cikin gida da kuma masu kiran lambobin wayoyin kasashen waje.
A wurin tattauna batun dokar dai, wakilan kamfanin MTN sun nemi a maida haramcin mallakar layin waya zuwa daga shekaru 14, amma ba a amince ba.