Gwamantin Tarayya ta ɗora laifin hare-hare, kashe-kashe da kwasar dukiyoyin da aka yi a Legas, lokacin Tarzomar #EndSARS kan ƙungiyar IPOB, wadda Nnamdi Kanu ke jagoranta.
Ya ce su ne kuma duk su ka kai hari Fadar Babban Basaraken Legas, Oba Rilwan, su ka kwashe kayan gidan, ciki har da kayan sarauta da sandar mulkin sa sunkutum.
A ranar Juma’a ce Minista Malami ya yi wa manema labarai wannan jawabi, dangane da mummunar aika-aika, ƙulle-ƙulle da zagon-ƙasa wanda Nnamdi Kanu da ɗan taratsin kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Igboho su ka riƙa yi.
Malami ya ce gogarman IPOB ne su ka kai wa Fadar Basaraken Legas farmaki, su ka fake da Tarzomar #EndSARS, su ka wulaƙanta fadar basaraken.
Sannan kuma ya ce akasarin hare-hare da kwasar dukiyar jama’a, duk aika-aikar ‘yan IPOB ce.
Haka nan an danganta hare-haren banka wuta da aka riƙa kaiwa gidaje da ofisoshi da hukumomi da ma’aikatun gwamnati a Lagos da wasu jihohi duk aika-aikar ‘yan IPOB ce.
Ya ce su ƙona wurare 150 a Lagos Terminal, sun ƙona gidan Gwamna Hope Uzordimma na Jihar Imo, kuma sun ƙone gidan Sanata Ndoma Egba a Kalaba, babban birnin Cross River.
Ya ce duk ƙunlle-ƙullen su Nnamdi Kanu ne domin yi wa ƙasar nan zagon ƙasan da zai hargitsa ta.
A ranar Alhamis dai an gabatar da Nnamdi Kanu a kotu, inda ya nemi kotun ta watsar da hutume-tuhumen da Gwamnatin Tarayya ke yi masa.
Babbar Kotun Tarayya ta ɗage sauraren ƙarar da aka gurfanar da gogarman neman kafa ƙasar Biafra, kuma Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, zuwa ranar 10 Ga Nuwamba.
Nnamdi Kanu a yau ta ƙarƙashin lauyoyin sa ya na ƙalubalantar cancantar tuhumar cin amanar ƙasa da ake yi masa a kotun.
A sabon roƙon da ya yi, ya nemi kotun ta yi watsi da shari’ar mai ɗauke da tuhume-tuhume bakwai da ake yi masa.
Babbar Mai Shari’a Binta Nyako ya ce a dawo ranar 10 Ga Nuwamba, bayan da ofishin Antoni Janar ya yi gyare-gyare ga caje-cajen da ake yi masa.
Daga nan ta bada umarnin cewa a bar mutum uku su riƙa ziyarar Kanu a kowace ranar Alhamis.
“Kuma shi Kanu ɗin ne da kan sa zai zaɓi waɗanda ya ke so su ziyarce shi.
Har yanzu dai Kanu ya na tsare a Hedikwatar SSS. Sai dai kuma roƙi kotu ta maida shi gidan kurkuku, amma kuma Mai Shari’a Binta Nyako ba ta amince ba.
Tun da farko dai SSS sun gabatar da Kanu a kotu, inda aka haye da shi a sama kan neme na biyar a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, misalin ƙarfe 9:45 na safe.
Sun isa ya na tsakiyar karta-kartan jami’an tsaro, kowane ɗauke da bindiga.
An hana ‘yan jarida da dama da lauyoyi da dama shiga harabar kotun.
A ranar Litinin ne Ofishin Antoni Janar ya gyara tuhume-tuhume da Gwamnatin Tarayya ke yi wa Kamu, daga biyar zuwa bakwai.
Daga cikin caje-cajen da ake yi masa har da cin amanar ƙasa, yi wa ƙasa zagon-ƙasa, maƙarƙashiya da kuma ayyukan ta’addanci.