Domin kawo karshen rikice-rikice tsakanin fulani makiyaya da manoma gwamnatin jihar Gombe ta hana makiyaya ratsawa ta jihar da dabobin su har sai manoma sun kammal girbin amfanin gonakinsu a jihar.
Hakan na daga cikin abubuwan da aka tattauna a zaman da gwamnan jihar Inuwa Yahaya ya yi da jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki a jihar ranar Juma’a a fadar gwamnati.
A wani takarda da kakakin gwamnan jihar Ismaila Misilli ya raba wa manema labarai, gwamnati ta ce za ta kyale makiyaya su fara shiga jihar daga watan Janairu 2022.
Kwamishinan yada labarai na jihar Julius Lapes ya yi kira ga manoma da su girbe amfanin gonan sun da wuri sannan kada kuma kada su kona gonakin su saboda dabbobi da za su zo kiwo.
Lapes ya ce gwamnati ta hana sa yara kiwon dabbobi sannan za a rika fita kiwo ne daga karfe 6 na safe zuwa shida na yamma a jihar daga yanzu.
Ya kuma ce gwamnati ta rage tsawon dokar hana walwala da ta saka domin dakile yaduwar cutar korona daga karfe goma na dare zuwa biyar na safe zuwa daga 12 na dare zuwa biyar na safe.
Gwamnati ta umurci jami’an tsaro da su kama duk mai tuka keke napep ko dan acaban da abin hawansa bai da rajista.